
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya magantu kan ƙarin farashin man fetur inda ya gabatar da jawabi wa ƴan Nijeriya alhali ya na ƙasar Chana.
Tinubu ya ce hakan da ma wasu gyare-gyare da gwamnatinsa ke yi na daga cikin salon haɓaka tattalin arziƙin Nijeriya, ya na mai cewa su na bin hanyoyin da suka dace wajen cimma hakan.
Mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya hakaito inda shugaban ƙasar ya ke cewa, “mene ne ɓangaren ƙamarin da zai kai mu wajen, idan ba za mu iya jure wa tsauraran matakan da za su buɗe hanya wa ƙasarmu mai albarka da ƙwarewa ba?”
“Gwargwadon yadda ku ke son komai kyauta, sai ya ƙara tsada, kuma a samu jinkirin samun ci gaban da ake buƙata,” inji shi.
A ranar Talatar da ta gabata ne, Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya ɗage farashin litar man zuwa N855 a gidajen sayar da mansa wanda hakan ya sabbaba wa mutane yin dogayen lauyaka don sayan mai.
Hakan ya sanya al’umma da dama kokawa game da sabon hukuncin a halin matsi da al’umma ke ciki inda suka nemi gwamnatin ta sake nazari game da hakan.
Yayin wani zama a Beijing, Tinubu ya kare hukuncin da cewa tsauraran matakai su na taimakawa matuƙa wajen samun ci gaba a tattali.
Ya ƙara da cewa, duk da cewa akwai wahalar samun amincewa tsakanin al’ummar ƙasa, a shirye ya ke ya yi amfani da tsauraran matakan wajen ciyar da Nijeriya gaba.
