
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ce Ma’aikata masu katin shaidar ɗan ƙasa ne kaɗai za su amfana yayin da ta shirya fara sayar da ton 30,000 na shinkafa.
Ministan Albarkatun Noma, Abubakar Kyari a lokacin ƙaddamar da tsarin ya ce an yi haka ne don a toshe ƙofar yin ha’inci ga masu saya da kuma taimakawa wajen rage farashin kayan abinci a Nijeriya.
Kyari, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu, ya ce kowane ma’aikaci damar sayan buhu ɗaya kadai aka ba shi.
Sannan, za a sayer da kowane buhu ɗaya mai nauyin 50kg akan N40,000 kamar yadda aka sanar a baya.
Ya kuma yi kira ga al’umma su bada haɗin-kai yayin gudanar da ayyukan cin gajiyar shirin wanda musamman gwamanti ta samar da shi ne don rage raɗaɗin matsi da al’umma ke ciki akan abinci.
