Matsalar abinci: Ambaliyar ruwa ta lalata hekta sama da 115,000 a Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Nijeriya na ci gaba da fama da matsalar ƙarancin abinci, yayin da sabbin bayanai daga cibiyar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEOC) suka nuna cewa ambaliyar ruwa ta lalata gonaki sama da hekta 115,000 a faɗin ƙasar.

Jihohi 29 da ƙananan hukumomi 154 ne abin ya shafa, inda sama da mutum 611,000 lamarin ya shafa kai tsaye, mutum 225,169 suka rasa matsugunansu, gidaje 83,457 ne suka lalace, mutum 201 ne kuma suka rasa rayukansu sannan mutum 2,119 kuma suka samu raunuka a bana.

Wannan bayanin na ambaliya ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da ƙarancin abinci da kuma ƙaruwar hauhawar farashin kayan abincin, wanda hukumar ƙididdiga ta Nijeriyan (NBS) ta bayyana ya hau sama da kashi 40 cikin 100.

Wani sabon bincike da Babban Bankin Nijeriya CBN ya gudanar daga ranar 22 zuwa 26 ga Yulin 2024 ya nuna cewa, hauhawar farashin kayayyaki zai tilastawa magidanta a Nijeriya kashe mafi yawan kuɗaɗen shigarsu kan abinci nan da watanni shida masu zuwa.

By ukarofi