Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Mai taimaka wa Shugaban ƙasa kan Dabarun Sadarwa, Mista Bayo Onanuga, ya ce, kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ya amince cewa ya na fama da matsalar kuɗi wanda hakan ya sa ba zai iya ci gaba da bayar da tallafin man fetur ba.
Mista Onanugu, mai ba da shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru ga Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana hakan a cikin wani saƙon da ya wallafa a ranar Talata a shafin ɗ.
Ya ce idan hukumar ta NNPC ta ci gaba da biyan kuɗaɗen tallafin man fetur, kamfanin zai iya shiga fatara.
Onanuga ya ce bashin da NNPC ke bin kamfanin ya samo asali ne sakamakon ƙoƙarin da kamfanin ke yi na rage tsadar man fetur da kuma kare masu amfani da shi a Nijeriya, maimakon duk wata yaudarar gwamnati.
“NNPC ta yi kuka a kwanan nan saboda ba zai iya ci gaba da ba da tallafi a kan man fetur ba,” inji shi.
“Babu zaɓi mai sauƙi. Dole ne a yi wani abu da zai sa NNPC ya tsira, a kuma ci gaba da tafiyar da hanyoyin gwamnati don samun sauƙ.
A cewar Onanuga, za a kuma samu raguwar buƙatuwar musayar kuɗaɗen waje na shigo da man fetur daga aasashen waje.
Tun da farko dai hukumar ta NNPCPL ya ƙara farashin man fetur zuwa naira 855 kan kowacce lita, amma kuɗin ya kai kusan N1,200 a wasu gidajen mai.
