Gwamnatin Ogun ta rufe wasu kamfanonin Chana saboda rashin tsafta

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Jihar Ogun, ta rufe wasu kamfanonin ƙasar Chana guda biyu bisa zarginsu da gudanar da ayyuka a gurɓatattun muhalli da kuma zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba gwamna shawara na musamman kuma Manajan darakta na OGWAMA, Abayomi Hunye ya fitar a ranar Lahadi.

Kamfanonin da abin ya shafa su ne – Yibao Industrial Limited, wanda ke ƙauyen Bara da ke kan titin Sagamu – Abeokuta da kuma Ronchang Industrial Park, ɗaura da farfajiyar Julius Berger, a kan titin Legas zuwa Ibadan.

A cewar gwamnati, kamfanonin sun ƙi shigar da masu sharar da aka amince da su don sarrafa sharar su yadda ya kamata, wanda hakan ya saɓa wa sashe na 17 na dokar hukumar kula da shara ta jihar Ogun ta shekarar 2020.

A yayin da yake jagorantar tawagar tabbatar da rufe kamfanonin, mai ba da shawara na musamman kuma Manajan Darakta na Hukumar Kula da Sharar ta Jihar Ogun (OGWAMA), Honorabul Abayomi Hunye ya ce OGWAMA ba ta da wani zaɓi illa ta rufe kamfanonin guda biyu bayan an yi musu gargaɗi da su tsaftace muhallinsu, sun gaza, kuma sun cika wuraren nasu da shara wanda ya saɓa wa sashe na 17 na dokar sarrafa shara ta jihar Ogun 2020.

Kamfanonin biyu an kuma same su da laifin shigar da sarrafa sharar da ba a amince da su ba wajen kwashe sharar su, wanda ya saɓa wa sashe na 17 na dokar hukumar kula da sharar ta jihar Ogun na shekarar 2020 da kuma ci gaba da hana masu sharar da aka sanya su kwashe daga cikin shararsu. kayan aiki tun 2021.

An kuma same su da laifin zubar da shara a hanyar Sagamu-Abeokuta da Legas zuwa Ibadan ba bisa ka’ida ba.

Hunye ya ce, “babban dalilin rufe kamfanonin shi ne a tabbatar da cewa sun bi ƙa’idojin sarrafa shara a jihar.

“Mun ba su sanarwa da gargaɗi da yawa kuma sun ƙi ji. Har ma mun je harabar su domin a duba su da dama domin mu ba su shawarar su tsaftace muhallinsu da kuma shigar da masu sharar da gwamnati ta amince da su, amma ba su yi kasa a gwiwa ba.

“Dukkan su biyun sun haɗa da masu kwasar shara wazanda ba su da ikon sarrafa sharar su wanda hakan ne ya sa matsugunin su ke da datti wanda hakan ke sanya mazauna jihar warin da ba dole ba da kuma yiwuwar kamuwa da ruwa a karkashin kasa daga sharar da ba a kula da su ba.

“Saboda haka, ba mu da wata hanya da ta wuce mu rufe su domin cimma muradun jama’a, saboda halayensu da ayyukansu na nuna rashin mutunta hukuma musamman daga kamfanonin da ‘yan kasashen waje suke da jahannama wajen lalata mana muhalli.

“Ba za mu naɗe hannayenmu mu kalli waɗannan kamfanoni su na lalata jiharmu ba, wanda ba mu isa mu gwada a ƙasarsu ba.”

Don haka Hunye ya yi kira ga kamfanonin da su ma suke da laifi irin na kamfanonin ƙasar Chana, amma har yanzu ba a kama su ba a jihar Ogun, da su yi aiki a cikin dokokin jihar ko kuma su kasance a shirye a sanya musu takunkumi.

By ukarofi