Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta ƙasa (N-HYPPADEC), Abubakar Sadiƙ Yelwa, ya yi gargaɗin cewa Dam ɗin Dadi Kowa a Jihar Gombe na daf da rugujewa.
Don haka ya yi kira da a ɗauki matakan gaggawa don daƙile bala’in da ke kunno kai wanda a yanzu ya zama barazana ga mutane da al’ummomin da ke zaune a kewayen wurin.
Yelwa ya bayyana haka ne a ranar Litinin a taron manema labarai a hedikwatar N-HYPPADEC da ke Minna.
Ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-ɓaci a kan iftila’in ambaliyar ruwa, yana mai cewa barazanar ta addabi al’ummomi da dama a jihohi 28 na tarayyar ƙasar nan.
“A cewar rahoton da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta fitar, a bana, ambaliyar ruwa ta kashe kusan mutane 200, tare da raba sama da mutane 208,000 da muhallansu a jihohi 28 daga cikin 36 na ƙasar, tare da lalata gidaje da filayen noma da yawa,” inji Yelwa.
Da yake ƙarin haske game da yanayin madatsar ruwan Dadi Kowa, manajan daraktan ya bayyana fatansa na ganin an shawo kan bala’in, inda ya ƙara da cewa gwamnati ta tattara kwararrun da suka dace domin duba madatsar ruwan.
Ya ce, “Ina sane da cewa gwamnatin tarayya ta tattara kwararru domin duba madatsar ruwa daga ma’aikatar ruwa da na muhalli.”
A nan take, ya ce dam ɗin na iya buɗe hanyar da ba za ta kara jefa rayuwar al’ummomin da ke ƙarƙashinsa cikin hadari ba.
Ya koka da cewa kashi 80 cikin 100 na jihohin da bala’in ambaliyar ruwa ya fi shafa sun fito ne daga shiyyar N-HYPPADEC sakamakon wuraren da suke da ayyukan samar da wutar lantarki da ake yi a waɗannan jihohin.
Ya ce, “Rahoton farko da jami’an mu suka fitar ya nuna cewa a jihar Binuwai ya zuwa yanzu al’ummomi 634 ne lamarin ya shafa tare da wanke filayen noma kusan 30,000, a jihar Kebbi, gidaje 6,959 sun lalace tare da wanke gonaki kusan 10,000.”
Yelwa ya bayyana matu1ar godiya ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, bisa taimakon gaggawar da ya bayar wajen bayar da umarnin sakin kuɗaɗen tallafin ga jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa a bana, inda ya ƙara da cewa, “wannan zai taimaka matuƙa wajen tallafa wa waɗanda abin ya shafa a wannan mawuyacin lokaci.”
