Ana ci gaba da jimamin rasuwar Wakilin Manhaja na Gombe, Mohammed Ali

Spread the love

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Ana ci gaba da jimamin rasuwar Wakilin Blueprint Manhaja a Jihar Gombe, Malam Muhammed Ali, wanda ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya. Marigayin, wanda ya rasu yana da shekara 70 a ranar Talata, 27 ga Agusta, 2024, ya bar matar aure ɗaya da ’ya’ya takwas.

Muhammed Ali, tsohon ɗan jarida ne wanda ya shafe tsawon shekarunsa yana aikin jarida. Haifaffen garin Jos ne a jihar Filato, asalin Kanuri daga garin Dikwa a jihar Borno. An haife shi a ranar 10 ga watan Janairu, shekarar 1955.

Marigayin ya halarci Makarantar Firamare ta Nur-Ud-Deen dake garin Jos daga shekarar 1960 zuwa 1965, sannan ya tafi makarantar sakandare ta Craft School dake Soba, Zaria, jihar Kaduna, daga shekarar 1966 zuwa 1968. Daga nan ya wuce GTTC Bukuru a jihar Filato daga shekarar 1969 zuwa 1971, inda ya samu shaidar karatu ta (Higher School Certificate, HSC).

Bayan haka, ya samu damar shiga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria (ABU) a Samaru, jihar Kaduna, inda ya yi kwas na satifiket kan ayyukan kula da dakin karatu (In-serɓice Library Duties Certificate Course) daga shekarar 1972 zuwa 1976. Sannan ya tafi Jami’ar Maiduguri inda ya yi General Basic Reporting Course daga shekarar 1986 zuwa 1987. Daga nan kuma ya tafi Jami’ar Jos inda ya karanci aikin jarida na Adɓanced News Reporting and Editing Course (Post-Graduate Diploma eƙuiɓalent) daga shekarar 1988 zuwa 1989.

Marigayin ya yi ayyuka daban-daban a rayuwarsa. Daga shekarar 1973 zuwa 1976, ya zama ma’aikaci a dakin karatu na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria (ABU). Bayan haka, ya zama babban jami’in saye da sayarwa na General Sales Representatiɓe, Paiko and Partners Ltd, a Itapeju Apapa, jihar Lagas, daga shekarar 1977 zuwa 1980.

Aikin Jarida:

Muhammed Ali ya fara aikin jarida da jaridar National Concord da Amana inda ya zama wakilinsu a jihar Legas, a matsayin jami’in sadarwa (Radio Communicator) daga shekarar 1980 zuwa 1984. Daga baya ya zama wakilin jaridar National Concord da Amana a jihohin Borno, Adamawa, da birnin tarayya Abuja daga shekarar 1985 zuwa 1990. Daga nan ya koma jaridar Sunray Newspapers a jihar Patakwal, inda ya zama wakilin jaridar a jihar Filato har zuwa shekarar 1992.

A shekarar 1996 zuwa 1998, Muhammed Ali ya koma jaridar The News Magazine a jihar Legas, sannan ya zama wakilin jaridar Triumph Newspaper ta gwamnatin jihar Kano a matsayin babban wakili (Senior Reporter). Daga nan ya koma jaridar TELL Magazine a jihar Legas a matsayin jami’i kuma marubuci mai kula da shiyyar Kano (Bureau Chief) daga shekarar 2000 zuwa 2005.

A shekarar 2006 zuwa 2014, ya koma jaridar NEWSNOW Magazine wadda ake wallafa ta a jihar Adamawa, inda ya zama shugaban yankin arewa (Northern Bureau Chief). Daga shekarar 2014 zuwa 2018, ya kasance Edita na jaridar Arewa A Yau da ake wallafa a jihar Gombe, sannan daga shekarar 2019 zuwa 2021, ya kasance wakilin jaridar Aljazirah Nigeria a jihar Gombe.

A rayuwarsa, marigayin ya kasance mai son karance-karance, rubutu, da kuma tafiye-tafiye.

Zantawa da ‘Ya’yan Marigayin:

Wakilinmu ya samu zantawa da babban dan marigayin, Shu’aibu Muhammed Ali (Dan Asabe), mai shekara 42, inda ya bayyana cewa ya ji zafin rasuwar mahaifinsa domin tun daga lokacin da aka sanar da shi rasuwar, bai iya bacci ba, har kwana biyu bai iya cin abinci.

Dan Asabe ya ce mahaifinsu yayi jinya ne na kwanaki shida kafin Allah ya karbi ransa. Kafin rasuwar sa, mahaifinsu ya kira shi ta waya ya gaya masa cewa ko bayan ransa ya rungumi kannensa su kuma rike zumunci. A cewarsa, kasancewar mahaifinsu yayi yawo sosai saboda aikin jarida, suka nemi su zauna waje daya don kada karatunsu ya samu matsala.

Dan Asabe ya yi kira ga gidajen jaridun da mahaifinsu ya ke aikewa da labarai kafin rasuwarsa, da su dinga tunawa da iyalansa. Yace zai yi kyau a samar da wata Gidauniya ta Muhammed Ali wacce za ta amfanar da jama’a da iyalansa, domin ya bada gudunmawa sosai a jaridun kudu da arewa.

Shehu Usman Muhammed Ali (Shagari), dan marigayin na biyu, ya ce rasuwar mahaifinsu ta girgiza su sosai. Yaso ace Allah ya hada su kafin rasuwar mahaifin nasu, amma hakan bai yiwu ba. Shagari ya ce mahaifinsu ya basu tarbiya mai kyau har suka yi karatu suka zama manya, kuma sun so su saka masa kafin rasuwarsa, amma Allah ya fi sanin dai-dai.

“Wata rana muna hira da shi ya taba gaya min cewa, daga yawon aikin jarida da yayi a Najeriya, jiha daya ce kawai bai je ba a cikin jihohi 36 da Abuja,” inji Shagari.

Marigayi Ali yi jinya a asibitin ƙwararru na Jihar Gombe, an kuma yi jana’izarsa a asibitin, sannan aka binne shi a makabartar Musulmi da ke kan hanyar Gombe zuwa Bajoga.

By ukarofi