Tare da BUSHIRA NAKURA
08099263283
DSI Yusuf Abubakar jami’in Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya ne kuma ɗan asalin Jihar Zamfara, amma mazaunin Jihar Kano. A tattaunawarsa da Wakiliyar Blueprint Manhaja, BUSHIRA NAKURA, ya bayyana ma na yadda rayuwa ke kasancewa da kuma burinsa a nan gaba. Ga yadda hirar ta kasance:
MANHAJA: Assalamu alaikum warahamatullah wabarakatuhu. Mai karatu zai so jin cikakken sunanka da sunan da aka fi saninka da shi, kafin tarihinka a takaice.
ABUBAKAR: Amin waalaikumussalam warahamatullah wabarakatuhu. Sunana Yusuf Abubakar, amma wasu suna kira na da sunan garinmu, watau Maradun. An haife ni a cikin ƙaramar Hukumar Maradun da ke cikin Jihar Zamfara, na yi karatun firamare a garin na Maradun, inda daga nan na wuce makarantar gaba a garin Wurno da ke Jihar Sokoto, daga nan kuma na je wata kwaleji da ta ke a Akwanga cikin Jihar Nasarawa.
Bayan na kammala na je na yi karatun computer a ABU Zaria bayan na kammala na samu aikin computer a wani Company Multi System da ke Abuja daga nan kuma na dawo jahata ta Zamfara inda na samu aiki a Political Affair cikin goɓernment House.
Daga nan kuma na samu aiki a Hukumar Shige da Fice ta ƙasa. Na yi aure kuma Allah Ya albarkace ni da ‘ya’ya.
To a yanzu me aka sa a gaba sana’a ce ko aikin gwamnati?
Ni ma’aikacin gwamnati ne a karkashin hukumar shige da fice ta ƙasa, watau Nigeria Immigration Serɓice…
Ina kake da zama; Kano ko Zamfara?
A yanzu Ina zama ne a Jahar Kano.
Shekarar ka nawa ka na aiki tare da Hukumar Shige da Fice ta ƙasa?
Na samu kimanin shekara 14 zuwa 15 ina aiki da wannan hukumar.
Wane mataki kake yanzu?
Ina matakin Mataimakin Sufuritanda watau (DSI.)
Me ya baka sha’awa cikin wannan aikin?
Abin da yake ba ni sha’awa a wannan aiki na farko yanda suke gudanar da aikinsu da ilimi da kuma iya hulɗa da jama’a, na gida da na ƙasashen ƙetare, wannan na da alaƙa da wani horo da ake yawan yima ma’aikatan hukumar yanda zasu iya karɓar bakinsu. Ana kiran wannan horo (Hostmanship Training). A taƙaice kenan.
Wacce irin gudunmawa hukumar ku take bayarwa?
A gaskiya hukumar mu tana bada gudunmuwa sosai ta fanni daban daban kadan daga ciki akwai fannin tsaron ƙasa domin kula da shege da fice na baki, shiyasa idan kin lura jami’ar hukumar ne na farko a ko wacce iyakar ƙasa wato boda, domin sai ka cika sharuɗɗan da doka ta tanada kafin su barka ka shigo ƙasar.
Haka zalika hukumar ce ke da alhakin yima yan ƙasa masu sha’awar fita ƙasashen waje takardun da ya dace domin kare martabarsu a ƙasashen ƙetare. Sannan kuma ita ke da alhakin sa ido ga baƙin ƙetare da ke cikin ƙasa kamar yanda doka ta tanada. Da dai sauran abubuwa da dama da suka shafi sha’anin tsaron ƙasa da walwalar yanƙasa da kare martabarsu.
Me ya fi birge ka a aikinka?
Babban abinda ke birge ni a aikina shi ne in yi ma al’umma aiki suji daɗi su yiman addu’a, ina jin daɗin inji ance Allah Ya jiƙan iyaye Allah Ya kare ku Allah Ya sa a gama lafiya.
Kai a kan kanka wacce irin gudunmawar kake son badawa cikin hukumar ku?
Gudunmawar da nake son badawa ko nake badawa, Ina ba wannan hukumar gudunmuwa sosai kamar yanda tsarin mulkin hukumar ya tanada, misali fita aiki cikin lokaci da yin aiki tuƙuru da kuma riƙe amanar hukumar da ƙasa bakiɗaya.
Wane burin kake dashi wanda kake son ka cika shi?
Babban burina shi ne a turani aiki a ƙasar waje a ƙarƙashin wannan hukumar. Sai kuma fatan yanda na shiga wannan aiki lafiya Allah Ya nuna man na kammala lafiya da kuma fatan Allah Ya haɗa mu da alhairan da ke ciki Ya kuma kare mu da akasin haka.
Ko za ka iya faɗa mana irin gwagwarmayar da kasha a rayuwarka?
Gwagwarmayar rayuwa lam sai dai ince Alhamdulillahi domin a gaskiya gwargwado ansha gwagwarmayar rayuwa domin tun ina Primary 5 Allah Ya yi wa mahaifiyata rasuwa kinga ko dole ne asha gwagwarmayar rayuwa, kaɗan daga ciki shi ne lokacin da na gama secondary ina zama a gida na bi wani yayana da ke aikin mota muna zuwa Legas, Ondo, Osun, Benin da dai sairansu. Cikin hukuncin Allah mun samu haɗari da motar yakai sau biyu ko ma uku, na ƙarshen ne ya daga mani hankali sosai wanda muka yi a Dakatsalle mun dawo daga legas Inda aka samu mutuwa sosai a ciki harda abokin aikina Kabiru yayin da mu kuma aka kaimu a Assibitin Tiga daga baya aka dawo da mu assibitin Kura dukka dai a cikin Jahar Kano, amma saboda ƙurciya guduwa na yi daga assibitin na koma a motar ni ke yima kaina allura har na warke.
Daga baya na daina aikin motar na koma yin achaɓa ban taɓa bantawa wata rana bayan na dawo na gaji sai ga wani abokina yazo wurina yana tasi muna hirar rayuwa shi ne yake ceman yana fama na ce ai kai da sauƙi a mota kake shi ne ya ba ni key ya ce ga shi inje na yi inji. Daga ranar na fara tasi duk da ban taɓa kan mota na yi tafiyar kilo mita ɗaya ba, amma a haka na fara tasi har na iya mota sosai da passenger wannan shi ne sanadiyar tasi a cikin gwagwarmayar rayuwa da na yi.
Da Allah Ya kawo ƙarshen tasi ɗin kuma na haɗu da wani Balaraben Sudan ana cemasa Dr. Umar Yakub daga ɗauko sa yake ce man yana son ya sayi mota zan iya koya masa. na ce ya saya zan iya mana. A kwana a tashi ya sa yi mota na fara koya masa duk wata yana biyana, wata rana ya ce za mu je Legas haka kuma aka yi bayan munje Legas muka dawo Abuja shikenan dai ba mu Legas ba mu Taraba ba mu Kano da Maiduguri har Allah Ya kawo ƙarshen zamansa a Nijeriya a lokacin nake ce masa ya yafe min idan na yi masa wani abu marar sa kyau, ya ce babu Abin da na yi masa, ya ƙara da cewa da yanda nake haka sauran mutanen Nijeriya suke da ta wuce zagi a duniya.
Da zai wuce ya samar man aiki a wani company da ke Abuja daganan dai sai gani har a ɓilla. Watarana naje wajen wata yayata Dakta, da ke aiki a assibiti ziyara na gaya mata duk abubuwan da ke faru shi ne ta ce to ba inda zani in ba makarantaba ta nema min adiminshin a College of Education Akwanga kuma ta bani mota 505 domin in Riƙa zuwa makaranta. A kwana a tashi na kammala karatuna bayan na dawo gida a Zamfara, zama kuma ya dawo wata rana na samu Naira dubu biyar na bi wani yayana ana ce masa Dan ma’azu zuwa legas na sawo kayan gyaran waya na dawo gida na fara gyaran waya ba tare da wani ya koyaman ba cikin iyawar Allah da wannan sana’ar na yi aure kuma na riƙe iyalaina.
Ana haka sai kuma na samu aiki a Goɓernment House. Ina aiki a nan watarana wani director mu ana ce masa Alhaji Hambali ya ma rasu kwanan baya Allah Ya gafarta masa ya ce kana son aikin Immigration na ce masa e, shi ne sanadiyar shiga ta wannan aikin da nake ciki a yanzu. Wannan shi ne taƙaitacen gwagwarmayar rayuwa da na samu.
Shin Bayan wannan aikin da kake yi kanayin wata sana’ar ne?
Bayan wannan aikin ina noma da kiwon tantabaru wanda tantabarun sun zama kamar wani ɓangare na rayuwata domin har ta kai idan ba a ba su abinci ba har kan gadona suna zuwa. Ban mantawa akwai wata rana na dawo daga aiki suka yiman chaaa shi ne wata ‘yata ke ce masu munafukkai kun zo ku gaya masa ba a baku abinba ko. Wannan shi ne abinda nake yi bayan aikin gwamnati da nake yi a halin yanzu.
Me ye cikas ɗinka cikin wannan aikin naka?
Banda wani cikas a aikina kuma ina fatar kada Allah Ya kawoman wani cikas har na kammala.
Wane abu ne na farin ciki wanda bazaka taɓa mantawa da shi ba?
Babban abinda nake tunawa na ji daɗi shi ne, yanda na rabu da iyayena lafiya ba tare da nadamar wani abu marar kyau da na aikata masu ba. Wannan abu yana sani farin ciki sosai.
Wane abu ne na baƙin ciki wanda bazaka taɓa mantawa danshi ba?
A gaskiya banda wani abin Baƙin cikin da nake tunawa ya ɓata man rai domin na kasance mutun da baya da riƙon abu marar amfani a rayuwa.
Yanayin gari wanne kafi so damina sanyi da zafi?
A gaskiya ina son yanayin sanyi ban sani ba ko don na ɗan yi zama a Jos ne. Amma a gaskiya ina jin daɗin yanayin sanyi.
Wane irin kalar abinci da abinsha kafi so?
Ina son tuwo da miyar kuka da kuma koko da kosai.
Me yake saurin saka fushi?
Rashin cika alƙawari ba tare da wani uzuri ba.
Me ka fi so ga mutane?
Zama na tsakani da Allah komai za mu yi mu yi don Allah mu bari don Allah.
Meye baka so ga mutane?
Munafurci da ƙananan maganganu.
Me kafi so a yi ma kyauta dashi?
Addu’ar Allah ya jikan iyaye Allah Ya albarkaci zuri’a.
Ko akwai abinda kake son cewa wanda ya shafe ka ko al’umma wanda ba a tambaye ka ba?
Eh gaskiya akwi kaɗan daga ciki shi ne ina kira ga mutane da mu koma ga Allah kowa yasan abinda yake yi wanda ba daidaiba ya gyara mu taru mu gyara mu roƙi Allah Ya yafe mana. Matuƙar mun daina don Allah, Allah zai dubi halin da muke ciki ya tausaya mana idan kuma ba haka ba zai bar mu da dabararmu mu yi ta fama.
Su waye gwanayen ka a duniya ?
Gwanaye na a duniya su ne iyayena domin su ne sanadiyar zuwana duniya kuma suka ɗora ni akan tarbiya wacce nake alfahari da ita.
Wacce nasiha zaka yi wa matasa musamman cima zaune waɗanda ba su son nema?
Yanzu ai cima kwance sai mahaukaci, domin babu wanda zai nemo ya baka in baka tashi ka nema ba.
Don haka shawarata ga matasa ita ce ku tashi ku nemi na kanku yau in baka da shi ko magana ka faɗa a gida za a ɗaukeka kamar mahaukaci, sai kaga ƙannenka ya yi magana ta fi taka saboda bai zama cima kwance ba.
Ko kana da wanda za ka gaisar?
Ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki.
Ina yi ma Jaridar Blueprint Manhaja Hausa fatan alhairi da kuma ƙara samun ɗaukaka domin maganar gaskiya babu wani labari da zaka samu a jaridar Blueprint Hausa wanda idan ka karanta ba za ka ƙaru ba. Jarida ce mai nemo labarai lungu da saƙo domin mu masu karatu mu amfana. Daga ƙarshe ina yi mu su addu’ar Allah ya ƙara basira da ɗaukaka.
