Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
An yi kira ga ‘yan siyasa da kada su sanya siyasa a harkan tsaro musamman abinda ya shafi ta’addanci.
Dan majalisar wakilai Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya faɗi haka da yake hira da manema labarai a garin Daura wajen da aka gudanar da taron saurare da jin ra’ayoyin jama’a na shiyyar Daura.
Ya ce ya kamata al’umma da ‘yan siyasa su sani dole su tashi tsaye wajen magance tsaro a yankunan su ba kawai su zurawa wa gwamnati ido ba.
Dan majalisar da ke wakiltar Mashi da Dutsi a jihar Katsina ya faɗa cewa al’umma su suka san matsalar yankunan su saboda haka dole su yi aiki kafaɗa kafaɗa da jami’an tsaro wajen daƙile barazanar ‘yan ta’adda da sauran ɓata gari.
Ya yaba da matakan da gwamnatin Dikko Raɗɗa ke ɗauka wajen kawo zaman lafiya a jihar.
Haka kuma ya jinjina wa gwamnan akan ƙoƙarin sa wajan haɓaka harkan ilimi da samar da ruwan sha da kuma shimfiɗa sabbin hanyoyi da kyautata rayuwar al’ummarsa a faɗin jihar.
Majigiri wanda ɗan jam’iyyar adawa ta PDP ya ce ya amshi gayyatar gwamnatin Katsina a madadin jam’iyun adawa a jihar ya kuma miƙa ƙorafe-ƙorafe al’ummar yankunansu.
Taron da gwamna Dikko Raɗɗa ya jagoranta ya sami halartar mataimakinsa da ‘yan majalisar zartarwa ta jiha da kuma ‘yan majalisar dokoki ƙarƙashin kakakin majalisan na jihar.
An dai shirya taron ne a shiyar Funtuwa, Daura da Katsina domin saurare da jin ra’ayoyin jama’a game da kasafin kuɗi na 2025.
Haka kuma taron zai saurari ƙorafe-ƙorafen al’umma kan yadda Gwamna Dikko Raɗɗa ke tafiyar da harkokin gwamnati a jihar.
