Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Spread the love

Casemiro ya shirya tsaf domin ƙin amsa tayin kowacce ƙungiya, saboda ya lashi takobin mayar da martabarsa da ci gaba da kasancewa a Man United.

Newcastle ta haƙura da nacin ɗauko mai tsaron gida na Ingila, da ke taka leda a Crystal Palace Marc Guehi 25, domin nunawa ƙungiyar ba za a yi amfani da su idan an buɗe kasuwar musayar ‘yan wasa ba.

Mai tsaron gida na Sifaniya da ke taka leda a Real Madrid Dani Carɓajal, mai shekara 32, ya ce akwai yiwuwar zai buga ƙwallom ƙafa a Amirka kafin ya yi ritaya daga buga ƙwallo.

Everton na duba yiwuwar buɗe tattaunawa kan Daɓid Moyes a matsayin manajan ƙungiyar, shekara 11 bayan ɗan Scotland ɗin ya bar Goodison Park domin fara aiki da Manchester United.

Real Madrid na son ɗauko ɗan wasan Sifaniya mai taka leda a Manchester City Rodri, 28, wadda ke shirin ɗauko ɗan wasan tsakiya kafin ƙarshen kakar wasan nan.

Istanbul Basaksehir na cikin ƙungiyoyin Turkiyya hudu da ke son ɗaukar bashin mai tsaron gida na Ingila da ke taka leda a Newcastle Kieran Trippier mai shekara 33.

Galatasaray na son ɗauko bashin ɗan wasan tsakiya na Brazil Casemiro, mai shekara 32, sai dai dole Manchester United ta maida albashin fam 300,000 kan ɗan wasan a kowanne mako.

ƙungiyoyin Pro League na Saudiyya ka iya shiga zawarcin Casemiro a watan Junairu mai zuwa idan dama ta samu.

Liɓerpool na shirin buɗe hanyar tattaunawa kan ɗan wasan gaba na Masar Mohamed Salah, mai shekara 32, bayan ya sanar da cewa wannan ce kakar wasan shi ta ƙarshe a ƙungiyar, bayan nasarar da suka yi kan ƙungiyar Manchester United.

Manajan Pumas UNAM, Gustaɓo Lema ya ce ƙungiyar Liɓerpool ta so ɗaukar ɗan wasan da ke taka musu leda kuma na Meɗico Cesar Huerta, mai shekara 23.

Chelsea ta shirya domin bada ɗan wasan baya na Ingila Ben Chilwell, mai shekara 27, aro ga ƙungiyar Turkiyya, duk da cewa har yanzu ba bu wanda ya taya ɗan wasan.

ƙungiyar Chelsea da AEK ta Athens na tattaunawa kan ɗan wasan gaba na Iɓory Coast Daɓid Datro Fofana mai shekara 21, amma a matsayin bashi.

Tottenham ta kammala tattaunawa kan sayan ɗan wasan tsakiya na Amirka Johnny Cardoso, mai shekara 22 daga Real Betis, kan farashi fam miliyan 21. 

By ukarofi