NNPCL ya mayar da martani bisa kalaman MURIC kan farashin fetur

Spread the love

Daga BELLO A BABAJI

Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya yi tsokaci game da takardar da Ƙungiyar kare Ƴancin al’ummar Musulmi (MURIC) ta fitar inda ta ce matatar man fetur ta Ɗangote na fuskantar barazana game da burinta na samar da mai a farashi mai sauƙi ga al’umma.

MURIC ta tabbatar da cewa, ƙarin farashin mai da NNPCL ya yi a kwanan nan zai hana Matatar Kamfanin Ɗangote (DRL) bada man fetur a farashi mai sauƙi ga ƴan Nijeriya wanda an gina shi ne domin su amfana, wanda ta ce NNPCL ya mamaye baki ɗaya hajojin matatar.

Sai dai, cikin wata takarda da babban jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin, Olufemi Soneye ya fitar, NNPCL ya bayyana cewa farashin dangogin man fetur na kowacce matata ya ta’allaƙa ne da yanayin kasuwa, ya na mai cewa ƙarin farashin da aka samu bai da tasiri ga DRL ko kuma kowacce matata.

Ya ce, idan har hakan ya tabbata, to dama ce ga matatar ta ke sayar da manta a farashi mai sauƙi a kasuwar ƙasa.

Sannan, ya ce NNPCL ba zai taɓa yin zagon ƙasa ga kasuwancin da ya ke da kaso a ciki na biliyoyin Daloli ba.

Bugu da ƙari, babu alaƙa tsakanin farashi mai sauƙi da wata matata ta gida da kuma tsarin farashin kasuwannin duniya kamar yadda DRL ta tabbatar.

Don haka, MURIC a matsayinta na jagora ga al’umma ya kama ta ke tabbatar da gaskiyar al’amari da hujjoji kafin ta yi magana a kai.

By Babaji