Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’o’i ta ƙasa (JAMB) ta yi Allah-wadai da iƙirarin da ake na cewa tana da hannu a cikin shirin ɗaukar ɗalibai masu babbar difiloma (HND).
A wata sanarwa da kakakin hukumar Fabian Benjamin ya sanya wa hannu, ta ce hukumar ba ta da hannu, ko iko, ko kuma ta gudanar da ayyukan shigar da masu babbar difiloma HND.
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar ta JAMB ita ma ba ta da alhakin sauran shirye-shiryen manyan makarantu baya ga shigar da su a kai a kai.
Hukumar ta kuma ƙara da cewa ba ta san masu neman shiga HND ba kuma ba su da alaƙa da aikin JAMB.
A baya dai wasu ɗaliban HND sun zargi hukumar da laifin rashin zuwa yi musu hidimar bautar ƙasa wato NYSC.
An ce ɗaliban sun yi iƙirarin cewa ba a tara su aikin yi ba ne saboda sun yi wani shirin na wucin gadi na kammala karatunsu na ƙasa (ND).