LAFIYA UWAR JIKI: Cutar gyambon ciki (Olsa)

Spread the love

Masu karatu barkan mu da wannan lokaci. Sannunmu da sake saduwa a wannan shafi na Lafiya Uwar Jiki.

A rubutun da ya wuce na gabatar muku bayani kan yadda cutar Gyambon Ciki, wato Olsa, ke samuwa, sababanta da kuma mutanen da ke cikin haɗarin kamuwa da ita. Yanzu insha Allah zan ɗora daga inda na tsaya. 

Alamomin olsa:

Ciwon ciki (daidai tsakiyarsa). Wannan ciwon ciki ya na da wasu halaye kamar haka: ya kan zagaya bayan mutum, musamman idan olsar ta huda bangon tumbi na baya, ya fi tsanani da daddare ko lokacin da aka ji yunwa, kuma yana raguwa ko ƙaruwa idan mutum ya ci abinci. Ya danganta da bigiren da olsar ta kama. Idan olsa ta kama tumbin mutum ne, to cin abinci ya na tsananta ciwon; idan kuma sashen farkon ƙaramin hanji ta kama, cin abinci na rage raɗaɗin ciwon.

Haka kuma ciwon olsa ya na raguwa bayan mutum ya sha magani mai surka sinadarin asid da ke cikin tumbi wanda ake kira ‘antacids’.  

Yanayin ciwo ko raraɗin olsa shi ne mutum ya ji kamar ana ƙone wajen ko ana rura wuta.

Kaso 99 bisa 100 na masu fama da olsa su na yin wannan ciwon ciki. Kaso ɗaya ne jal ba sa yi. 

Jan hankali:

Akwai buƙatar mu fahimci cewa:-

Ciwon baya ba olsa ba ne

Yawan ɓacin rai ba olsa ba ne

Yawan faɗuwar gaba ba olsa ba ne

Yawan cin abinci ba olsa ba ne

Yawan fitsari ba olsa ba ne

Riƙewar ƙirji ba olsa ba ne

Cutuka masu kama da Gyambon Ciki:

Ciwon matsarmama ko tasawar matsarmama (Pancreatitis)

Ciwo ko tasawar maɗaciya {cholecystitis)

Sharrin olsa 

Idan olsa ta gawurta, ta kan kawo zubar jini ta ciki. Shi wannan gyambon da ta haddasa ai da shimfiɗar tumbi ce ko ta hanji, to yayin da ta addabi wajen, tana haɗawa da hanyyoyin jinin da su ka keto ta wajen. Hakan sai ya sa zubar jini.

Ta kan jawo rami. Saboda ita ƙwayar cutar olsa da ake kira H. pylori, ta na da kayan aikin da za su taimaka mata wajen kutsawa can cikin bangon tumbi ko na hanji.

Idan gyambon da olsa ta haddasa ya warke, to ya kan tattare, wanda a garin hakan sai ya ke fizgo shimfiɗar da ke kewaye da shi. Tunda hakan na faruwa ne a cikin abu mai kamar bututu ko payif (Pipe), mu tuna tun daga baki har dubura, payif ne wanda abinci ke wucewa ta ciki, shi wannan tabon sai ya takure hanyar wucewar abinci, ƙarshe ma ya toshe ta bakiɗaya idan babba ne.

Hanyoyin kare kai:

A kiyayi shan magugunan gajiya da ciwon gaɓoɓi irinsu Ibumol, Ibuprofen da Diclofenac ba tare likita ya rubuta maka su ba, domin sun a daga cikin sababan olsa.

A tsaftace hannaye bayan fitowa daga bayi. Ita kwayar cutar H. pylori za ta iya maƙalewa a hannu. Kuma za a iya ba wa wani ƙwayar cutar ta hanyoyi da yawa kamar taɓa wani abu ko taɓa abinci ko na sha. Allah ya kiyaye.

A guji shan giya da taba, saboda su ma suna jefa mutum cikin haɗarin samun olsa. Su na ɗaɗe shimfiɗar tumbi da ta hanji.

A kiyaye yin duk wani abu da zai iya tayar da ita (musamman masu olsa), misali cin yaji ko shan tsami ko gajiyar da jiki. Wahala ta na tayar da olsa ga waɗanda su ke da ita.

Ku ci gaba da bibiya ta domin samu sauran bayanai na lafiya insha Allah.

Naku, MIAbdullahi Mustapha Ibrahim Abdullahi

By ukarofi