Daga UNCLE LARABI
Shin sun yarda akwai wuta da aljanna kuwa? Wallahi idan da sun san akwai wannan da ba su iya barci a cikin na’urar sanyaya ɗaki ba har da munshari alhali talakawan da suke mulka na kwanaki babu abinci ba.
Na taɓa jin wannan labarin na King Fahad (Sarkin Makkah); ya ce, mafi girman nasarar da ya samu cikin mulkin da ya kwashe yanayi a Saudiyya shine, daidaita abincin basarake da mai kuɗi da talaka. Ma’ana; duk abincin da basarake ko mai mulki ko mai kuɗi zai ci, talakan Saudiyya shi ma irinsa zai ci.
Wannan ba wai ƙarya ba ne, domin har gobe duk wanda ya ziyarci ƙasa Mai Tsarki ya san cewar, talakan Saudiyya Shinkafa-Kaza da Labban Marai ya ke ci ya kuma sha. Sannan duk talaucinsa shi ma zai kwana cikin na’ura mai sanyaya ɗaki, kamar yadda mai kuɗi da mai mulki da basarake za su kwana.
Amma a Nijeriya fa? Kullum ƙara nesanta talaka da kayan jin daɗi da more rayuwa ake yi. Har yanzu a wannan mulkin zaluncin na Tinubu an fara nesanta talaka da abinda zai ci ko da maras daɗin ne ma.
Ba a bar talaka da rashin abinci kaɗai ba, an jefa ma sa tsoro da zaluncin rashin ba shi ilimi da rashin ba shi wutar lantarkin da ko da wayarsa ya samu ya yi caji ya haska wajen da zai kwanta.
A yau ɗin nan na haɗu da mutane barkatai da suke neman taimako kan abinda za su ci. Wasu maza ne magidanta majiya ƙarfi, amma an karya zuciyarsu da zaluncin talaucin da aka ƙirƙirawar wa ’yan ƙasar da gangan. Wasu kuma mata ne da yara ƙanana suna neman taimako, waɗanda da gaske sun yi kwana da kwanaki ba su ɗora tukunya ba.
Ina mahukuntan Nijeriya za su kai wannan zunubin na mafi girman zalunci da suka ƙaƙaba wa talaka na rasa yadda zai ci da kansa? Abinci yana fin ƙarfinsa. Wallahil azim akwai gidajen da ba za su ƙirgu ba a Nijeriya, musamman a Arewacin Nijeriya da sun daina ɗora tukunya. Masu dama-dama ne za ka samu su na iya yin girki sau ɗaya a rana.
Ya kamata mahukuntan Nijeriya su gyara tsari da salon mulkinsu ta yadda talakawan da suke mulka za su ji daɗi su san cewar, eh! su ma mutane ne kuma mahukuntan da suke mulkar su sun san haƙƙinsu da ya ke kansu.
Ina jiye wa mahukuntan Nijeriya ranar nadama! Ranar tonon asari! Ranar da Allah zai yi makamashin wuta da duk wani azzalumi.
Ya kamata daga yau ɗin nan ko daga yanzu, duk wani ɗan ‘Social Media’ ya mayar da hankali kan rubuce-rubucen jawo hankalin mahukuntan Nijeriya akan su kula da haƙƙin da ke kansu na talakawansu. Allah ya ɗora su ne akan talakawan, don su yi adalci, ba wai don su yi zalunci ba.
Ya Allah muna tawassali da kyawawan sunayenka tsarkaka ka kawo mana sauƙin wannan rayuwar da muke ciki. Ka ba mu shugabanni nagari masu adalci da jin ƙan bayinka albarkar Manzo Sallallahu Alaihi Wassalam. Amin summa amin.
Uncle Larabi marubuci ne a Kano mia cikakken sunan Abdullahi Jibril Larabi. Za a iya samun sa a wannan lambar waya 08065418892
