Tare da BASHIR MUDI YAKASAI
Rabon dukiyar ƙasa ya dogara ne ga irin tsarin mulkin da ’yan ƙasa suka amince a mulke su da shi, ƙasashen duniya akwai masu da’awar jamhuriyya, haka akwai masu da’awar mulukiyya, akwai masu muluka’u da kuma ’yan kasuwa da kuma kasuwa mai kawo riba.
Matsalar da Nijeriya da ’yan Nijeriya suke fuskanta shine sha’anin mulkin, su ba jamhuriyya ba, wato mulkin jama’a, su ce ga yadda za a yi a ƙasa, jama’a ne za su yanke, su ce ga yadda za a yi. Misali; dukiyar ƙasa ta man fetur da dangoginsa, su za su bayyana ga yadda za a haƙo ta, ga yadda za a tace shi, ga kuma yadda za a rarraba shi zuwa ga jama’ar ƙasa, domin kowa ya amfana daga wannan dukiya.
Da farkon fari kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka, dukiyar ƙasa ta wanda ya fara gano wannan dukiya ce, sannu a hankali sai wannan dukiya ta ƙasa sai ta koma hannun ’yan ƙasa da suka taru suna ɗibar amfanin wannan dukiya, kamar manomi duk abin da ya shuka ya kai shi ga girbi nasa ne ɗari bias ɗari. Idan gari ya zama gari, kowa yana da iko daga wannan fili ko jeji da ya share, domin noma ya zama nasa kuma duk abin da ya shuka a wannan fili nasa ne ɗari bisa ɗari.
Haka abu ya ke ga masu tono albarkatun ƙasa, kamar Kuza, Toma, Tagulla, Azurfa, Gorar Ruwa ko ma baƙin ƙarfe ko zinare da lu’u lu’u da kuma Mirjani da Tsakiya da ake tono su a teku har a zogaya shi da taɓo na yin tukwane da tangaran da sauran kayan ado na faɗi-ka-mutu.
Idan ana so a sami zaman Lafiya a ƙasar nan sai duk ɗan ƙasa ya san irin mulkin da za a riƙa mulkar sa da shi. Idan aka ce Dimukraɗiyya irin ta Amurka za a mulke shi da ita, to, sai ya san mene ne mulki irin na Dimukradiyya irin ta Amurka.
Ya sani cewa, mulki ne na “jari hujja”, wato mulkin na masu hannu da shuni. Tun daga kansila har zuwa shugaban ƙasa, mutane ne da za su zuba jarinsu, wato dukiyarsu, domin su sami damar sarrafa dukiyar ƙasa, su kuma su ba wa ’yan ƙasa la’ada daga ribar da suka samu.
Wannan shi ya sa ka ke ji su na cewa, ‘idan ka zaɓe mu za mu samar muku da aikin yi, za mu ba ku damar faɗar albarkin bakinku kuma ku na da damar kafa ƙungiyoyi da za ku tafiyar da rayuwarku’.
Wannan ta sanya ake bayar da damar a fito a yi zanga-zanga, amma ta zaman lafiya ba tare da ɓata dukiyar wasu ba ko ta gwamnati. Za ku faɗi dalilinku na yin zanga–zanga, domin goyon bayan jama’a. Saboda haka aka yi tsare–tsare ta yadda jama’a su sanya albarkacin bakinsu. Shi ya sa suke kiran mulkin dimukradiyya “mulkin jama’a domin jama’a”.
Amma a maganar gaskiya magana ita ce “Jari Hujja,”. Ka na da jari, ko da kai fasiƙi ne fajiri ne, madamfari ne, mayaudari, algungumi, ko da kuwa kai mazinaci ne, idan za ka buɗe shago da sunan cewa, kai ga sana’arka, ita gwamnati za ta kafa maka sharuɗɗa ta yadda za ka tafiyar da wannan sana’a ba tare da wanda ya zo sayar wannan hajar taka bai cutu ba, shikenan ka zama ɗan ƙasa na gari.
Saboda haka ta dimukaraɗiyya babu haramci wajen rabon dukiyar ƙasa ga dukkan wanda yake da wata basiri (Talent) da zai sarrafa ta ta zama dukiya. Amurka tana maraba da shi. Tsoronta shine tashin hankali (violence), kuma abokin gabarta shine ‘violent Person’, wato mutum mai son tashin hankali. Duk mutumin da zai ce bai yarda ba sai anyi ɗa’a (Morality) a sha’anin rayuwa, to, ka zama abokin gabarta, za su yi taron dangin su murƙushe ka.
Babban misali; duk shugaban da ya zo da tsarin cewa, dukiyar ƙasa ta ’yan ƙasa ce ya kamata ’yan ƙasa su amfana daga wannan dukiya, su ’yan dimukaraɗiyya zuciya, su kwaso mahaukata, masu gurɓataccen tunani su dagula al’amura domin kawai cigaba da kwasar dukiyar ƙasa da sunan ‘yan cin mallakar dukiya idan har ya zuba mata jari wannan jarin na basira ne ko na dukiya ta zahiri.
Wannan shi ya haifar da hana kamfanin NNPCL da sauran kamfanoni da suke ƙarƙashinsa, kamar matatun tace ɗanyen mai domin amfanin ’yan ƙasa. Masu ra’ayin tsarin mulkin dimukaraɗiyya za su taka rawar da suke so, domin su tabbatar dukiyar ƙasa ta zama tasu, da ’ya’yansu da jikokinsu. Wannan shi ya hana ’yan ƙasa su amfana daga dukiyar ƙasarsu. Matatun mai sama da sunan da ’yan dimukraɗiyya suka kira haramtattun matatun man fetur.
Amma matatunsu da suke yammacin Turai da Amurka ba haramtattu ba ne, domin su za su kwashi ɗanyen mai su kai waɗannan ƙasashe su tace su dawo mana da shi da farashin da su suka sanya, kuma mu ba su dama su rarraba shi daga farashin da suka tsara da sunan tallafi – ‘Subsidy,’ wanda Shugaban ƙasa ya ce ya soke daga ranar da aka rantsar da shi kan wannan kujera ta Shugaban ƙasa, wato Bola Ahmad Tinubu.
Idan aka bi dukiyar ƙasar nan tun daga lokacin da ƙasar Ingila ta tabbatar ƙasa nan ta koma hannunta a shekara ta 1912 suka shiga kakkafa dokoki na mulkin mallaka da mulkin mallake ƙwaƙwalen ‘yan ƙasa ta mayar da su ’yan takarda, wato elite, wanda ba su kai kashi biyar cikin ɗari, suka tilasta da cewa su ne masu ruwa da tsaki a al’amuran ƙasa, kuma duk wanda zai ja da su, to, ya zama ɗan ta’adda
Tun daga 1950 zuwa yau 2024, waɗannan ’yan takarda su ne za su ce ga yadda za a tafiyar da dukiyar ƙasa daga karatun da suka koyar da su. Saboda haka saye ƙwaƙwale shine roman dimukraɗiyya.
Da ɗa’a ko ta ƙwayar zarra ce tare da shi ba za a takarda suke cin karensu babu babbaka.
Saboda haka duk mai tallata a buɗe iyaka (boarder) a kawo kasuwar shunku da kasuwar tsaye da sunan (Consultancy), da tsari na ‘subsidy’, rangwame a noma da kiwo, da rangwame a fagen ilimi, rangwame a kayan masarufi da rangwame a tafiye-tafiye, wato dai duk wata kafa da take da tasiri da jama’ar ƙasa a sama mata gurbi da dukiyar za ta koma gare su, da sunan tallafi – rangwame.
Saboda haka mu na kira ga gwamnati ta Shugaba Bola Ahmad Tinubu da Kashim Shettima cewa su tsaya tsayin daka da cewa, ‘no going back’ daga suke tallafi kowanne iri ne, domin kuwa yaudara ce a fakaice, domin ƙahon zuƙar jinin ’yan ƙasa ne cikin hikima. Mu sani cewa, kayan aro ba ya rufe katara.
