
Daga BELLO A. BABAJI
Ƴan sandan farin kaya ta DSS ta sake fasfo ɗin shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Ƙasa (NLC), Joe Ajaero bayan ƙwacewa da ta yi a ranar Litinin da ta kama shi.
Wasu shugabannin NLC sun ce jami’an ba su samu wani abu da ke nuna cewa ya na da alaƙa da ta’addanci ba.
An kama Ajaero ne akan hanyarsa ta zuwa Burtaniya don halartar taron Ƙungiyar Kasuwanci (TUC) da aka shirya a Landan inda ya shafe kusan sa’o’i 15 a hannun jami’an kafin sako shi.
Ganin haka ya sa NLC ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin a sako mata shugabanta kafin ƙarfe 12 na dare wanda kuma haka aka yi daga baya.
