Ambaliya: Shettima ya tallafa da tirela 50 na shinkafa ga ƴan Maiduguri

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Talata ne Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ziyarci Maiduguri don jajenta wa al’ummar Borno kan ambaliyar tafkin Alau da ta ɗaiɗaita dubunnan mutane.

Shettima, wanda ya jagoranci tawagar Fadar gwamnatin tarayya, ya samu tarba daga gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum inda ya kai shi Fadar Shehun Borno wanda nan ma ambaliyar ta shafa.

Daga nan ne Mataimakin shugaban ƙasar ya garzaya zuwa sansanin Bakassi inda aka kai waɗanda suka rasa matsugunansu.

Ya bayyana musu cewa, gwamnatin tarayya za ta tallafa musu da tirela 50 na shinkafa.

Ya ƙara da cewa, gwamnati tare da haɗin-gwiwar Hukumar Raya yankin Arewa-maso-Gabas da wasu hukumomi za su tabbatar da mutanen da lamarin ya shafa ba su haura sati biyu ba a sansanin.

By Babaji