Mutane 15 sun mutu sakamakon ambaliya a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
.
Mamakon ruwan sama ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 15 a yayin da wasu 3,094 suka rasa muhallansu a wasu yankunan jihar Katsina.

Hajiya Binta Husaini wacce ita ce shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, ta sanar da manema labarai a ofishinta.

Ta ƙara da cewa, aƙalla mutane 21,481 ne suka samu raunuka a yayin aukuwar lamarin.

Haka kuma, gidaje 32,542 suka rushe a ƙananan hukumomi 32 da ke faɗin jihar.

Hajiya Binta ta bayyana ƙananan hukumomin Dutsinma, Daura, Kaita, Katsina da Batsari a matsayin waɗanda ambaliyar ta fi yi musu ɓarna.

Haka nan, ambaliyar ta shafi ƙananan hukumomin Malumfashi da Matazu.

Ta ce, wannan mamakon ruwan saman ya faru ne daga watan Agusta zuwa Satumba inda yanzu haka shugaban hukumar ta ce akwai tallafin gaggawa daga Bankin manoma da ya fara isowa wanda an fara raba wa waɗanda abin ya shafa.

“Kayayyakin kuwa sun haɗa da tallafin kuɗi na kayan gini da kayan abinci.”

Ta kuma ce, hukumar ta tattara bayanai na adadin waɗanda suka mutu da asarar da aka tafka waɗanda har ta tura wa gwamnatin jihar.

Hajiya Binta, ta yaba da yadda al’ummar jihar ke fitowa suna taimaka wa waɗanda iftila’in ya shafa.

By Babaji