‘Yan sanda 32 ke tsaron ƙauyuka sama da 200 a Katsina – Raɗɗa

Spread the love

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa, ya bayyana cewa rashin isassun jami’an tsaro da kayan aiki sun taka rawa wajen ta’azzar rashin tsoro da ake fama da shi a jihar.

A tattaunawarsa da tashar DW, gwamna Raɗɗa ya ce akwai ƙaramar hukuma mai ƙauyuka sama da 200 a jihar wadda ƴan sanda 32 ne kawai ke samar da tsaro ga al’ummar yankunan.

“A jihar Katsina akwai ƙaramar hukumar da ke da ƴan sanda 32. Bindigarsu guda tara ce, mai aiki kuma guda biyar ce, ƙaramar hukumar da ke da ƙauyuka kusan 200. Mazaɓu sama da goma. Ya za a yi ɗan sanda 32 ya tsare su?”

Gwamnan ya ce, ya na takaicin yadda ƴan bindigar da ba su wuce mutum biyar ko goma ba ke tarwatsa gari guda, a cewarsa idan al’ummar jihar suka cire tsoro, za su iya kama su da hannu.

“Idan matasa ɗari suka yunƙura suka nufi ƴan bindigar ko sun kai mutum 20 da sun fara harba bindiga ɗaya, biyu kafin su yi harbi na biyar an kama su da hannu”, Inji Raɗɗa.

Ya kuma ce, dalilin da ya sa gwamnatin jihar ta buƙaci al’umma su yi fito na fito da ƴan ta’addar, shi ne saboda babu wadatattaun jami’an tsaro a ƙasar nan da za su iya kare su.

A cewar gwamnan, ƙin yin fito na fito da ƴan bindigar bai hana ɓarayin yin garkuwa da mutane ko ma a kashe su a wani lokaci.

By Babaji