‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyar da soja uku a Zamfara

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda biyar da sojoji uku a wani mummunan harin kwantan ɓauna da suka kai a safiyar ranar Alhamis a ƙaramar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

An kai harin ne a daidai lokacin da jami’an tsaro ke rakiyar ma’aikatan kamfanin gine-gine na Setraco Nigeria Limited.

Wani majiyar soji ya tabbatar wa ‘yan jarida wannan mummunan al’amari, inda ya bayyana cewa jami’an tsaron ba su yi ƙasa a gwiwa ba a lokacin da ‘yan ta’addan suka buɗe wuta.

Wannan harin kwantan ɓaunan ya yi sanadiyar mutuwar jami’an tsaro takwas da suka haɗa da ‘yan sanda biyar da sojoji uku.

Sai dai kuma martanin da sojojin suka yi cikin gaggawa ya hana a ci gaba da samun asarar rayukan ma’aikatan Setraco da sauran jami’an tsaro.

Duk da wannan mummunan asarar da aka samu, majiyar ta ƙara da cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama yayin wannan harin kwantan ɓaunan.

Majiyar ya ƙara da cewa “‘Yan sanda sun kwashe gawarwakin ma’aikatan da ‘yan bindigan duka.”

Wannan lamari dai ya biyo bayan wani rahoto da aka fitar, inda ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka tare babbar hanyar Gusau zuwa Funtua a Jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da wasu matafiya da ba a tantance adadinsu ba.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Zamfara, Yezid Abubakar, ya tabbatar da sace mutanen a babbar hanyar, inda ya ce ‘yan sandan sun baza jami’ai zuwa wurin amma har yanzu suna jiran cikakken bayani kan adadin waɗanda abin ya shafa.

By ukarofi