Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jami’an tsaron al’umma(CWC) sun kama wata motar haya ɗauke da albarusai a tsakanin Katsina zuwa Batsari
Babban jami’in tsaro da ke kula da ƙaramar hukumar Batsari Ahmed sunusi Batsari ya bayyana haka a Katsina lokacin da ya gabatar da albarusan gaban kwamishinan harkokin tsaro da harkokin cikin gida Dr Nasir mu’azu Danmusa.
Yace motar da ke ɗauke da fasinja guda 17 jami’an sa sun tsaida sune akan hanyar Katsina zuwa Batsari.
Babban jami’in tsaron ya ƙara da cewa a lokacin da suke gudanar da bincike sai ya lura da ɗaya daga cikin fasinja baya cikin natsuwa.
Ya cigaba da shaidawa kwamishinan cewa ko da suka fita da fasinja su ka fara binciken mazauni sa kenan ya ranta ana kare.
Ya dai gabatarwa kwamishinan da albarusai guda 610 a cikin akwai na bindigan nan AK47 guda da kuma bindiga ƙirar magazine guda biyu.
Sai dai jami’in tsaro Ahmed Batsari ya tabbatar wa kwamishinan tsaron cewa har sun sami bayanin inda wannan mutumin yake da nan bada jimawa ba zasu kama shi.
Daga nan sai babban jami’in tsaron ya gargaɗi direbobin haya da su rinƙa tabbatar da duba kayan fasinja kafin su ɗauke sa domin a cewar sa irin waɗannan ɓatagari ke kaiwa ‘yan ta’adda makamai a daji.
Kwamishinan tsaro Dr Nasir mu’azu ya jinjina wa jami’an tsaron na al’umma da sauran hukumomin tsaro da suke a yankin da ta’addanci ke faruwa da irin namijin ƙokarin da suke na ɗaƙile aikace aikacen yan ta’adda da masu taimaka musu.
Yace gwamnati za ta yi duk abinda za ta yi na taimaka wa jami’an tsaron su ga sun kakkaɓe yan ta’adda don dawo da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arzikin yankunan da jiha baki ɗaya
