
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnatin Kano ta sanar da sabuwar ranar komawa makarantu domin cigaba da ɗaukar karatu a sabon zango na shekarar 2024/2025.
Daraktan wayar da kan al’umma a Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Ƙiru ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Ya ce, ɗaliban da ke makarantun kwana za su koma a ranar Lahadi, 15 ga watan Satumba, su kuma ɗaliban jeka ka dawo za su koma ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, 2024.
Makarantun da za a koma karatun sun haɗa da firamare, ƙaramar sakandire da kuma babbar sakandire mallakar Gwamnati da masu zaman kansu.
To sai dai kuma sanarwar ba ta bayyana dalilin da ya sanya Kwamishinan Ilimi na jihar, Alhaji Umar Haruna ya ɗage ainihin ranar komawa Makarantar ranar 7 ga watan nan ba.
Saboda haka, sanarwar ta buƙaci iyayen yara da su kiyaye ranar komawar ta hanyar bin ƙa’idar da aka sanya.
Bugu da ƙari, an kuma shawarci ɗaliban su guji komawa makarantunsu da abubuwa da aka hana don kiyaye bin doka da oda da ma samun damar cin gajiyar ilimin da suka je koya.
A ƙarshe, Gwamnatin ta sha alwashin sanya idanu a dukkan makarantun jihar ta hanyar yin zagayen gani-da-ido don tabbatar da komai ya na tafiya yadda aka tsara shi.
