Daga AISHA ASAS
Al’ummar Hausawan Afirka (AHAD) ta karrama Jaridar Blueprint da ke buga jaridun Turanci da ta Hausa Blueprint Manhaja da kuma Wakilinta na jihar Kano Ibrahim Hamisu, a ranar makon Hausa ta duniya da ake gabatarwa a duk ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara.
A yayin da ya ke miƙa takardar ƙwarewar, Shugaban Al’ummar Hausawan Afirka Sardaunan Agadas AMB (Dr.) Abdulƙadir A. Koguna ya bayyana cewa, ganin irin gudunmuwar da Jaridar Blueprint ta ke bayarwa wajen bunƙasa da yaɗa harshen Hausa a Nijeriya.
Ya ƙara da cewa Ibrahim Hamisu kuwa mutum ne jajirtaccen da a ko da yaushe yake bada himma wajen ganin an inganta yadda ake amfani da harshen Hausa a cikin al’umma.
Daga nan (Dr) Koguna ya jaddada buƙatar da ke akwai wajen koyi da Jaridar Blueprint wajen bunƙasa harshen Hausa da kuma ingantattun labarai.


