Hankalin jama’a ya tashi da tashin farashin fetur

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Haƙiƙa hankalin ’yan ƙasa ya tashi da sabon tashin farashin man fetur. Tamkar duk lamuran yau da kullum ta tattalin arzikin ’yan Nijeriya na da alaƙa ta kusa ko nesa da man fetur. In ka debe kuɗin shiga da a ka bayyana hukumar kwastam na tarawa har yanzu ɗanyen man fetur ne babbar hanyar samun kuɗin shiga na Nijeriya. Ga dai sauran arzikin da ƙasar ke da shi ta fuskar noma, kiwo da ma’adinai amma hankali ya koma kan man fetur. Jihohi ma masu arzikin fetur kan samu wani kaso na musamman daga rabon arzikin ƙasa da hakan kan sa su zarra wajen samun ƙarin biliyoyin Naira duk wata. Wannan ya sa yankunan da ke da arzikin ɗanyen fetur kan matsa lamba don a haƙo man da hakan zai sa su shiga jerin jihohi masu samun kaso mai tsoka. Mu tuna yadda gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya koka kan yanda gwamnatin Nijeriya ko a ce masu haƙƙin cigaba da aikin rijiyoyin man fetur na Kolmani tsakanin Gombe da Bauchi da biris da aikin alhali har ƙaddamar da rijiyar fetur tsohon shugaba Buhari ya yi. 

Kazalika shi kan sa shugaba Tinubu tun ya na kamfen ya ziyarci bigiren da mara baya ga aikin. Jihohin biyu na tsayin daka don ganin an tabbatar fara fito da man da sayar da shi don jawo arziki yankin su. Ba wani ɓoyayyen lamari ba ne yadda wasu ma’abota jihohin da ke da arzikin man fetur ke ɗaukar sauran jihohi a matsayin kaska mai shanye jini har ma su ke ganin sauran jihohi ba za su iya rayuwa ba sai ta hanyar kason kuɗin fetur. 

Tarihi da a ke kawowa da nuna da kuɗin fatu, gyada da audugar arewa a ka gano man fetur a kudanci bai shalli irin waɗannan mutanen ba don ba sa ma ko sauraron wannan a matsayin wata gudunmawa. A zamanin mulkin marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua sai da ta kai ga gwamnatin ta yafewa tsageran Neja Delta masu fasa bututun mai da ma sace shi. Wannan dabara ta sa gwamnatin ta samu salama inda hako fetur da sayar da shi ya zama cikin sauƙi don a kan biya tsageran maƙudan kuɗi da sunan su ne masu gadin rijiyoyin man. A baya da zarar gwamnati ta so yin wani sauyi sai tsagera su yi barazana ɗaukar matakin hana haƙo man. Har yanzu ma a kan gano matatun man fetur na gargajiya da ɓarayin fetur ke kafa inda su ka tsoni man fetur ɗin daga bututun man zuwa matatun na su. 

Ba mamaki gwamnati na barin waɗannan don a zauna lafiya duk da ta na ganin su ta na’ura. Manyan kamfanonin fetur ma na duniya na jin daɗin aikin su a Nijeriya don wadatar man da yadda yarjejeniyar da a ka yi da su kan zama kwalliya na biyan kuɗin sabulu. Mai binciken nan na harkar kuɗi Dokta George Uboh ya sha miƙa bayanai na zargin yadda kamfanonin ƙetare kan kaucewa biyan harajin da ya dace ga gwamnati. Uboh ya mika takardun bayanan ga hukumar tara kuɗaɗen shiga FIRS da kuma majalisar dokokin Nijeriya. Mai binciken ma ya baiyana gaban kwamitin majalisa ya yi bayani filla-filla kan binciken da ya gano. Ba mu da labarin ko an dau wani mataki kan zargin ko kuwa shiru ka ke ji wai shaho ya ci shirwa. An lissafa Nijeriya a matsayin ta shida mafi arzikin fetur a duniya kuma fitattun ‘ya’yan ta sun jagoranci kungiyar ƙasashe masu arzikin fetur wato OPEC da su ka haɗa da marigayi Rilwanu Lukman da Muhammad Barkindo. In mun zaiyana rayuwar ƙasashe masu arzikin fetur da rayuwar ‘yan Nijeriya sai mu ga akwai bambanci na koma bayan tattalin arziki da Nijeriya ke fama da shi don maƙudan kuɗin da a baya ta ke kashewa kan tallafin fetur din da a ke shigowa da shi daga ketare da gaza raya matatun man cikin gida.

Alƙawuran raya matatun fetur na Fatakwal, Kaduna da sauran su na zama abun da ya gagari Kundila. Nijeriya ta zama kaza da kan kwan kan dami ba cin moriya. Matuƙar Nijeriya ba za ta iya tace man da jama’ar ƙasar ta ke buƙata ba, haka za a cigaba da kwallo da ƙasar a kasuwar sayen tataccen fetur na duniya.

Farashin litar man fetur a gidajen mai da ke ƙarƙashin kamfanin mai na NNPCL a Abuja ya koma Naira 897.

Wannan ya biyo bayan fargabar da kamfanin ya nuna na barazana ga iyawar sa ta samar da fetur a cikin gida saboda jibgin bashin da a ke bin sa.

Yayin da gidajen mai da dama ke rufe, gidajen na NNPCL na sayar da man ga dogayen layukan motoci.

Tuni matasa masu sayar da man a jarka su ka buɗe kasuwar su inda su ke sayar da lita kan kimanin N1400-1500.

Haƙiƙa tuni farashin sufuri ya ƙaru inda mutane su ka kara afkawa ƙunci.

ƙungiyar ƙwadagon Nijeriya NLC ta yi dirar mikiya kan gwamnatin Tinubu biyo bayan ƙarin farashin fetur daga Naira 617 zuwa Naira 897 a farashin hukuma.

NLC ta ce wannan tamkar cin amanar yarjejeniyar karin mafi ƙarancin albashi ne zuwa Naira 70,000.

An wayi gari a jiya Talata gidajen man da ke karkashin kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL sun ƙara farashi da fiye da  N250 in a ka yi la’akari da yanda a ka sayar da man a gidaje daban-daban.

Ma’abota motoci sun yi cirko-cirko ko su bi dogon layi su sha a farashin gwamnati ko kuma su saya a bakar kasuwa da ɗan Karen tsada daga Naira 1400-1500.

NLC a sanarwa ta ce ta amince da ƙarin Naira 70,000 a mafi ƙarancin albashi da alƙawarin ba karin farashi don gwamnatin ta ce in ta ƙara albashin mafi ƙaranci zuwa Naira 250,000 to lita za ta koma Naira 1500-2000.

NLC ta ce ba za ta lamunci barazana ba kuma ta na kira a dawo da farashin yadda ya ke gabanin yarjejeniyar.

Komred Nasiru Kabir jami’in ƙungiyar kwadagon ne “da sun yi yunƙurin wani abu ina mai tabbatar ma ka wallahi za mu shiga zanga-zanga ta ƙasa baki ɗaya kuma za mu shiga yajin aiki yanzu ma maganar da na ke da kai dinnan mun riga mun sanar da INTERNATIONAL LABOR ORANIZATION ILO, saboda haka ba za mu zuba ido ‘yan siyasar nan su na yi wa mutane abun da su ka ga dama ba gwamnatin mun lura ba sa son su ji wai an ce ga wata ƙungiya ta na faɗa da su ko kuma a na faɗa da zaluncin da su ke yi wa mutane a ƙasa da kuma babakere da almundahana”

Gwamnatin Bola Tinubu na nanata cewa harkar fetur ta zama kasuwa ne ke yin halin ta don ba batun tallafi duk da a na raɗe-raɗin ba da tallafin.

Abdul’aziz Abdul’aziz shi ne mai taimakawa shugaba Tinubu kan labaru “man fetur ya zama kamar kowace irin haja, dan kasuwa zai iya zuwa ya saya kamar yadda kasuwa ta kama zai ɗora ribarsa ya sayar a kai. To abun da ya ke faruwa kenan. Su ’yan kasuwa su za su je su sayo man fetur yanzu a kasuwar duniya su yi dakon sa su kawo gida a rarraba da motoci zuwa gidajen mai daban-daban wannan ne ya ke ba da alkaluman a nawa ne kowace litar mai za ta tashi, ba wai abu ne da gwamnati ke zama ta yanke ba”

NLC ta ce har zuwa yanzu ba a fara biyan mafi ƙarancin albashin ba na N70,000 wanda dama bai isa ba sai ga sabuwar magana.

Haƙiƙa akwai kwararan alamun da ke nuna ’yan Nijeriya na ɗaukar sabbin matakai wajen kaucewa dan Karen tsadar fetur.

Musamman tun sake tashin gauron zaɓin man mutane ke kawo shawarin bin wasu hanyoyi masu sauƙi da za su rage dawainiyar sayan fetur din.

Masu dan sukuni na tunanin juya injunan motocin su zuwa aiki da iskar gas duk da akwai tsadar juyawar.

Wasu kuma tuni sun fara tallata neman motoci kanana da ba sa shan man fetur da yawa don in sun sha su dau kwanaki su na cin moriya.

Haka kuma wasu na ba da zaɓin sayen babura da ke aiki da lantarki da kuma kekuna ko laulawa irin na zamani kamar yadda hatta a kasashe masu cigaban masana’antu a ke amfani da su.

Matakan na jama’ar kasa musamman masu ƙaramin ƙarfi bai zama da mamaki ba don yadda farashin fetur ɗin ba shi da tabbas.

Duk da matasa sun gudanar da zanga-zanga kan neman dawo da tallafin fetur amma miyagu iri su ka birkita; wannan ƙarin farashi ya nuna rashin tasirin zanga-zangar.

Kammalawa;

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya ce ya na cikin matsalar kuɗi da hakan ke barazana ga samar da wadataccen man a ƙasar. Bayanan kamfanin na nuna masu samar da mai na duniya na kaucewa ba da man a kan bashi don su na bin NNPCL bashin kimanin dala biliyan 6. Shin yaya a ka yi bashin nan ya taru haka kuma ko ƙarin farashin fetur na yanzu zai sa a iya biyan bashin don samun maslaha? Sai mu yi ta bin bayanai daga masu wuƙa da nama.

By ukarofi