Gwamnan Zamfara ya raba magungunan sama da biliyan N1 da kayan agaji na gaggawa ga asibitoci a jihar

Spread the love

Daga BELLO A BABAJI

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da aikin raba magunguna da kayayyakin kariya na kai-da-kai (PPE) da na bada agajin gaggawa ga asibitoci a jihar.

A ranar Alhamis ne aka gudanar da haka a asibitin cutukan sanyi (IDH) a Damba da ke Gusau, babban birnin jihar.

Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris acikin wata takarda da ya fitar, ya ce aikin na ɗaya daga cikin ababen da gwamnatin jihar ta shirya don inganta zamantakewar al’ummarta.

Ya ce, magungunan sun kai na adadin sama da Naira biliyan ɗaya waɗanda aka raba wa ɓangaren harkar lafiya don bunƙasa shi.

A lokacin da ya ke jawabi a taron, Gwamna Lawal ya bayyana aikin a matsayin salo na ɗaukar matakan kariya ga kula da marasa lafiya yadda ya dace.

Gwamnan ya yi kira ga ilahirin masu-ruwa-da-tsaki da suka haɗa da hukumomin gwamnati da likitoci da jagororin al’umma da su haɗe kai wajen gudanar da ayyukan don tabbatar da samun nasarori a shirye-shiryen da ya tsara don amfanin al’umma da ma jihar baki ɗaya.

Kazalika, ya buƙaci al’ummar jihar su yi amfani da damar da gwamnatin ta bayar ta yadda za su kula da lafiyarsu cikin tsari da kuma ƙoƙarin dakatar da bazuwar cutuka a tsakanin su.

By Babaji