An koro ‘yan cirani 400 zuwa gida Nijeriya daga Dubai 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mahukuntan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun tiso keyar ‘yan Nijeriya 400 sakamakon zama a ƙasar ta yankin gabas ta tsakiya ba bisa ka’ida ba.

Wannan mataki na zuwa ne makonni bayan dawo da bayar da biza da ƙasar ta yi ga ‘yan NNajeriya.

Rahotanni sun ce manyan hukumomin ƙasar da suka haɗa da na agaji da mai kula da ‘yan cirani da masu kula da shige da fice da kuma hukumar yaƙi da safarar mutane baya ga jami’an ofishin babban mai bayar da shawara kan sha’anin tsaro na Nijeriyar ne suka tarbi mutanen a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja fadar gwamnatin ƙasar.

Kamar yadda kafofin yaɗa labaran Nijeriyar suka ruwaito, mutanen 400 sun ƙunshi mata 90 da kuma maza 310 waɗanda bayanai suka ce wasunsu izinin zamansu a ƙasar ta Haɗaɗɗiyar daular Larabawa ya ƙare amma suka ƙi ficewa yayin da wasunsu suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

Galibi ‘yan Nijeriyar kan yi amfani da damar shiga ƙasar da nufin karatu ko kuma cinikayya amma sai su juye zuwa ƙwadago ba tare da takardun izinin yin aiki ba.

Haka zalika akwai bayanan da ke alaƙanta ‘yan Nijeriyar da aikata ba daidai ba a ƙasashen musamman na gabas ta tsakiya lamarin da a lokuta da dama kan kaiwa ga korosu gida.

By ukarofi