Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Mataimakin Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsin Ma FUDMA, Farfesa Armayau Bichi, ya nemi ɗaukacin sanatoci da sauran shugabanni da masu riƙe da muƙamai da masu wadata da sauransu kan su yi koyi da mataimakin shugaban Majalisar Dattijai ta ƙasa kuma Sanata mai wakiltar Kano Arewa, DSP Sanata Baro I Jibrin, kan ɗaukar nauyin ɗalibai kimanin 500 a Jami’ar FUDMA da ke Jihar Katsina a nan gida Nijeriya da kuma ɗalibai guda 70 da DSP Barau Jibrin ya raba musu takardun samun guraben yin karatun digiri na biyu a jami’o’in wajen Nijeriya domin yin karatu a fannoni muhimmai na karatu da Nijeriya da duniya ke buƙatar fannonin wanda DSP ya ɗauki nauyinsu, kamar dai yadda Farfesa A.Y Bichi ya bayyana hakan a ranar Litinin da ta gabata a ɗakin taro na Ammani da ke Kano.
Ita ma Hon. Hajiya ‘Yardada mai Kano Bichi, tsohuwar Kwamishiniyar Al’amuran mata ta Kano kuma ɗaya daga cikin masu ba DSP Barau I Jibirin shawara don ci gaban al’umma ta ce kullum burin DSP al’umma ta samo bunƙasar ilimi, lafiya, noma da sauran fannonni na cigaban Kano, da ma Nijeriya baki ɗaya, a cewar Hon. ‘Yardada Mai Kano Bichi.
