Sinner ya zama ɗan Italiya na farko da ya lashe US Open

Spread the love

Lamba ɗaya a wasan ƙwallon Tennis a duniya, Jannik Sinner ya doke Taylor Fritz, inda ya lashe US Open, Grand Slam na biyu a shekarar nan.

Dan ƙasar Italiya, wanda ya zama zakaran Australian Open a Janairu, ya yi nasara a kan ɗan Amurka da cin 6-3 6-4 7-5.

Ya yi wannan nasarar kwana 19 tsakani, bayan da aka wanke shi da soso da sabulu, sakamakon da sau biyu a watan Maris aka samu sinadarin kara kuzarain wasa a jininsa.

Sinner ya ɗaga hannu sama ya kalli sararin sama, wanda ya zama ɗan Italiya na farko, bayan Guillermo ɓilas a 1977, wanda ya fara lashe Grand Slam biyu a karon farko a kaka ɗaya.

Haka kuma Sinner shi ne daga Italiya da ya lashe gasar da ake yi a Flushing Meadows ta ɗan wasa ɗaiɗai.

Shi kuwa Fritz ya barar da damar zama ɗan Amurka na farko da ya zama zakara tun bayan shekara 21.

Dan Amurka na ƙarshe da ya ci US Open shi ne Andy Roddick a 2003.

By ukarofi