PDP ta dakatar da Dino Melaye kan ayyukan zagon-ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kogi, ta dakatar da ɗaya daga cikin manyan ƴaƴanta, Dino Melaye kan zarginsa da ayyukan zagon-ƙasa.

Dino, wanda tsohon Sanata ne, an dakatar da shi ne daga Gunduma ta ɗaya ta Ayetoro Gbede bayan ƙin amsa gayyatar da aka yi masa.

Jagoran Gundumar na jam’iyyar ya ce an dakatar da shi ne sakamakon yin ayyukan da suka shafi zagon-ƙasa da kuma zarginsa da rashin yin biyayya.

Haka nan, an yi hukuncin ne yayin nazari game da rahoton kwamitin ladabdtarwa na jam’iyyar wanda aka wakilta ya yi bincike akan zargin da ake ma sa.

Hakan ya faru ne kwanaki kaɗan bayan da Dino Melaye ya yi zargin cewa jam’iyyar tasu ta zama ta kuɗi, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

An ga inda ya zargi shugaban jam’iyyar na riƙon ƙwarya, Iliya Damagum da Sakataren shirye-shirye, Umar Bature da wargaza PDP acikin rubutun nasa.

By Babaji