Obasanjo da AbdulSalami da Gusau sun yi zama da IBB a Minna

Spread the love

Daga BELLO A BABAJI

Tsoffin shugabannin Nijeriya, Olusegun Obasanjo da AbdulSalami Abubakar tare da Janar Aliyu Gusau, sun ziyarci tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) a gidansa da ke Minna a jihar Neja.

Wani da ke da kusanci da ziyarar ya ce, manyan ƙasar huɗu sun gudanar da zama ne na sirri wanda ya ɗauki tsawon sa’a guda inda daga nan ne Obasanjo ya fice daga garin.

Ya ce, zaman nasu bai rasa nasaba da lamuran ƙasa da suka shafi tattali wanda hakan ya jefa al’umma cikin matsin da su ke fuskanta.

Ya kuma ce, mutane 10 ne ƴan rakiyar Obasanjo waɗanda su na isa garin, ba tare da wata-wata ba suka je gidan IBB yayin da sauran mutane biyun suka same su a can.

Kawo yanzu dai ba a san musabbabin haɗuwar tasu ba yayin da ake sa ran hakan na da alaƙa da lamuran da suka shafi al’umma.

By Babaji