
Daga BELLO A BABAJI
Aƙalla mutane huɗu ne suka rasa rayukansu a ƙaramar hukumar Yola ta Arewa da ke Jihar Adamawa sakamakon ɓarkewar cutar kwalara.
Kantoman ƙaramar hukumar, Barista Jibril Ibrahim ya tabbatar da hakan wa manema labarai a ranar Lahadi inda ya ce hakan ya shafi gundumomin Alkawa, Ajiya da Limawa waɗanda yanzu haka akwai mutane 40 da ke karɓar kulawa a babban asibitin Yola game da lamarin.
Ya ce, jami’an lafiya na cigaba da kula da yanayin tare da nuna buƙatar taimako daga gwamnatin jihar, ya na mai kira ga al’umma su taimaka wa likitoci a ƙoƙarinsu na dakatar da yaɗuwar cutar.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su ruwaito duk wani bayani na alamar cutar a inda su ke gami da kiyaye ababen da ka iya haifar da ita.
A lokacin da ya ke magana game, Kwamishinan Lafiya na jihar, Mista Felix Rangwami ya ce sun karɓi samfurin ruwan kuma su na gudanar da bincike a kai yayin da su ke jiran sakamako daga ɗakin bincike, don haka ba za su ce akwai ɓarkewar cutar ba a jihar kai tsaye.
