
Daga BELLO A. BABAJI
Hedikwatar Tsaro, DHQ ta ce ta samu labarin wani faifan bidiyo da ke yawo inda a ciki ake zargin an tsare wani jami’in sojan ruwa mai suna Abbas Haruna na tsawon shekaru shida ba bisa adalci ba.
Cikin wata takarda da Daraktan Labarai na rundunar, Burgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, DHQ ta tabbatar wa al’umma cewa jami’an tsaron Nijeriya za su cigaba da aiki da adalci da bin dokar ƙasa.
Ya ce, kotun rundunar ta kan tabbatar da yin adalci da bada dama ga waɗanda aka zalunta gami da yi mu su adalci a yadda dokar sojoji ta samar.
Game da batun zargin, Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa ya yi umarnin a gaggauta gudanar da bincike wanda da zarar an kammala, za a sanar da al’umma sakamako.
Rundunar ta kuma yi kira ga al’umma su ƙaurace wa yaɗa labaran da ba su da tabbas a kai yayin da ake cigaba da bincike.
Ta kuma tabbatar mu su da cewa za su bayyana sakamakon nan ba da jimawa ba cikin adalci.
