Mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya buƙaci shugaban PDP na Jihar Edo Anthony Aziegbemi ya janye zargin ya yi masa kan zaɓen gwamna da za a yi a jihar.
Aziegbemi dai ya zargi gwamnatin tarayya da shirin yin magudi a zaɓen, inda ya ce Malam Ribadu ya bayar da dala miliyan biyu ga ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen.
A cikin takardar ranar 15 ga Satumba, 2024, lauyoyin Malam Ribadu, Charles Musa & Co, sun bayyana zargin a matsayin “ƙarya ce kwata-kwata” kuma sun buƙaci a janye shi cikin gaggawa.
Lauyoyin sun bayyana mutuncin Malam Ribadu da jajircewarsa na yaƙi da cin hanci da rashawa a matsayinsa na ɗan sanda a aiki, kuma shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC. Sun ɗauka cewa “ba zai yiwu ba ya sa hannun shi cikin irin waɗannan ayyukan.
Don haka Ribaɗu ya buƙaci Mista Aziegbemi da ya ba shi hakuri a bainar jama’a tare da janye labarin gaba daya.
Ya kuma buƙaci a buga bayanin janyewar a cikakken shafi a aƙalla jaridun ƙasar guda biyar, shafukan labarai na yanar gizo goma da gidajen talabijin na ƙasa da ƙasa guda bakwai.
Hukumar ta NSA ta kuma buƙaci a biya Naira biliyan 10 a matsayin diyya.
Bugu da ƙari, lauyoyin sun sanar da shugaban jam’iyyar cewa rashin biyan buƙatun a cikin kwanaki bakwai na iya tilasta musu ɗaukar wasu matakai, wanda zai iya haɗa da daukar matakin shari’a don tabbatar da kare haƙƙin Malam Ribadu.
