Yadda farashin fetur zai kasance a NNPCL bayan ɗibar farko daga matatar Ɗangote

Spread the love

Daga BELLO A BABAJI

Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya ce zai sayar da kowacce litar fetur a Arewacin Nijeriya a farashin sama da N1,000 bayan yin jidon farko daga matatar Ɗangote.

Kakakin NNPCL, Olufemi Soneye ya faɗi hakan a ranar Litinin cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya yi bayanin yadda farashin zai kasance la’akari da jihar da ake sayar da shi.

A Jihar Borno, za ake sayarwa ne akan N1,019 yayin da a jihohin Abuja, Sakkwato, Kano da makusantansu, za a ke sayarwa a N999.22.

A Oyo da Ribas da sauran jihohin Kudu kuma, za ake sayarwa ne akan N960.

Sai kuma jihar Legas da makusantanta inda za ake saya a mafi ƙarancin farashi na N950.

Soneye ya ƙara da cewa, an tsara farashin ne ƙarƙashin dokar masana’antar man fetur, ya na mai bayyana cewa man da suka yi dako a ranar Lahadi, sun saya ne da Daloli wanda shi ne na watan Satumba.

Ya ce, a ranar 1 ga watan Oktoba, 2024 ne za su fara sayan man daga matatar da kuɗin Nijeriya, wato Naira.

Kazalika, ya ce matuƙar aka samu rangwame daga matatar ta Ɗangote, to abu ne da za a yi godiya a kai inda ya ce za su tabbatar hakan ya kai ga al’umma.

A ranar Lahadi ne matatar Ɗangote ta musanta sayar wa NNPCL fetur akan N898, duk da cewa ba ta ayyana nata jaddawalin farashin ba.

By Babaji