Dakatar da ni da PDP ta yi wasan yara ne – Sanata Tsauri

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Tsohon Sanata, Umar Ibrahim Tsauri ya bayyana dakatar da aka yi masa daga jam’iyyar PDP a matsayin kodai wasan yara ko kuma anyi ne da gangan don a tozarta shi.

Yayin da yake mayar da martani game da batun dakatar da shi da jam’iyyar ta yi a matakin gundumar Tsauri wadda nan ne mazaɓarsa, ya ce kawo yanzu bai samu takardar dakatarwar ba, ya na mai cewa ya yi magana ne don yawan kiransa ta waya da akai tayi daga ko’ina a faɗin ƙasar nan.

Ya ce a matsayinsa na wanda ya yi Sanata ya kuma riƙe muƙamin sakataren jam’iyar ta ƙasa da kuma zama ɗan kwamitin amintattu na jami’iyyar, kwamitin zartarwa na ƙasa ke da hurumin ladaftar da shi.

Jam’iyyar PDP a matakin gunduma ko ƙaramar hukuma ko jiha, babu wanda ke da ikon dakatar da shi ko koransa a jam’iyyar kamar yadda tsarin mulkin jam’iyyar ta tanadar.

Tsauri ya ce shekarunsa 74 da haihuwa don haka ba shi da sha’awar yin takara ko riƙe muƙami a PDP sai dai ya na nan a jam’iyyar har sai idan ta kore shi.

Tsohon Sakataren jam’iyyar ya zargi shugaban jam’iyyar na jiha, Nura Ahmadi kurfi da yi wa shugabannin jam’iyyar na gundumar Tsauri yaudara da rufa-rufa.

Ya ce, shugaba da Sakataren da suka sa hannun a dakatarwar sun faɗa wa shugaban jam’iyyar na jiha inda ya kira su zuwa Katsina tare da roƙansu da su taimaka masa wajen sasanta tsakaninsa da Sanatan don a tafi tare.

Amma daga baya sai aka fito da farar takarda aka rubuta sunayensu da lambar wayarsu aka basu suka sanya hannun su 14, aka bai wa kowanne Naira dubu ashirin.

Sannan, Sanata Tsauri ya ce ba shi da matsala da Nura Ahmadi kurfi domin ya yi wa mahaifinsa manaja har na tsawon shekara 35, ya na mai cewa bai taɓa samun matsala da shi ba.

“Kuma shi Nura yayi aiki karkashi na a lokacin ina sakataren jam’iyar na ƙasa, domin haka wannan danbarwar ba tsakanina da Nura Ahmadi ba ne da uwar jam’iyyar ta ƙasa ne don kawai na ce ayi abin da shi ne dai-dai.”

Da ya ke magana, Sakataren jam’iyyar na gundumar Tsauri Abdullahi Garba ya ce shi bai sa hannu a takardar ba, kuma ma bai ga takardar dakatarwar ba balle a ce ya sa hannu.

By Babaji