Tinubu ya je Maiduguri jajen ambaliya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya je garin Maiduguri, babban birnin Borno don jajenta wa gwamnatin jihar da mutanenta kan ambaliyar da ta auku a makon da ya gabata.

A ranar Lahadi ne Shugaba Tinubu ya dawo Nijeriya daga Landan wanda zai duba matakin ɓarnar da ambaliyar ta yi a gidaje, asibitoci, kasuwanni, makarantu da sauran kadarorin al’umma.

Bayan isarsa babban filin jiragen sama na Maiduguri ne, gwamnan jihar, Babagana Zulum da wasu manyan jami’an gwamnati suka tarbi shugaban ƙasar.

Hukumar bada Agaji ta Gaggawa ta ce, ambaliyar ta shafi kusan rabin birnin bayan mamakon ruwan sama da fashewar wani sashi na madatsar Alau da aka samu.

Hakan ya yi sanadiyar damejin ababe da dama ciki har da makarantu da asibitoci da makamantansu.

Sannan, wasu fursunoni sun tsare yayin da aka samu rushewar wani sashi na ginin kurkukun da su ke da kuma arcewar wasu namun daji sakamakon buɗewar gidan ajiyar dabbobi na Sanda Kyamiri.

By Babaji