Har yanzu ɗan uwa ga Wike shi ne kwamishinan zaɓen Edo – INEC

Spread the love

Daga BELLO A BABAJI

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC ta yi watsi da kiran da jami’yyar PDP ta yi mata na a sauya kwamishinan zaɓe na Edo, Anugbum Onuoha yayin da ake ƙara kusantar zaɓen jihar da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba, 2024.

A baya ne jam’iyyar PDP ta buƙaci a sauya Onuoha daga muƙamin kwamishinan zaɓen kasancewar ya na da alaƙa ta jini da Ministan Abuja, Nyesom Wike wanda su ke hasashen zai iya amfani da shi wajen cimma wata manufa.

Cikin wata takarda da shugaban jam’iyyar na jihar, Anthony Aziegbemhin ya aika wa shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce kusancin da ke tsakanin Wike da kwamishinan, ba abin a yi shuru ba ne a kai wanda Wike da kansa ya tabbatar da cewa su na da alaƙa a wata hira da aka yi da shi.

A lokacin da ya ke magana game da batun, Sakataren Labarai na shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi ya yi kira ga jam’iyyar ta mayar da hankali wajen bin ƙa’idodin zaɓen, ya na mai cewa ba za a sauya kwamishinan zaɓen ba.

Ya ƙara da cewa, za a gudanar da zaɓen ne a mazaɓu 4,519, ba a ofishin kwamishinan ba, sannan akwai hanyoyin tantancewa na zamani, don haka babu maganar sauya shi.

By Babaji