
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon shugaban rundunar sojojin ƙasa na Nijeriya, Laftanal Janar Theophilus Yakubu Ɗanjuma ya ƙalubalanci jagororin tsaro su kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci da suka addabi sassa daban-daban na ƙasar.
TY Ɗanjuma ya bayyana haka ne a lokacin gabatar da wani littafi mai suna ‘Big Boots: Lessons from My Military Service’ wanda Manjo-Janar Solomon Udouma ya wallafa, da aka yi a ɗakin taro na sojoji da ke Abuja.
Ya ce, a halin yanzu babu wani uzuri da za a bai wa jami’an kan halin taɓarɓarewar tsaro da ke cigaba da addabar Nijeriya.
TY, wanda tsohon ministan tsaro ne, ya yaba wa ƙoƙarin sojoji wajen samar da haɗin-kai da daƙile barazanar tsaro a sassa ƙasa.
Ya ce, akwai buƙatar dakarun su ƙara zage damtse wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya kuma yi godiya ga manyan hafsoshin tsaro ganin yadda su ke bai wa jami’ansu kulawa musamman bayan ajiye aiki.
A lokacin da ya ke magana a taron, Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya ce jami’an tsaron Nijeriya za su cigaba da tsare aikinsu da kyautatawa kuma a bisa tsarin da ke tafiya da zamani.
