Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi jihohi 11 yayin da Kamaru ta saki ruwa daga dam ɗin Lagdo

Spread the love

A ranar Talata ne gwamnatin Tarayya ta fitar da sanarwa game da shirin da ƙasar Kamaru ke yi na sakin ruwa daga madatsar ruwa ta Lagdo. Wannan sanarwar ta fito ne da sa hannun babban daraktan hukumar kula da ayyukan ruwa ta Nijeriya (NIHSA), Umar Muhammed.

A cewar sanarwar, hukumomi a madatsar ruwa ta Lagdo za su fara sakin ruwa daga ranar Talata 17 ga Satumba 2024.

Sakin ruwan zai gudana ne a hankali daga mita 100 cikin daƙiƙa 100 m^/s wanda zai kai 1000 a hankali cikin kwanaki bakwai.

Da wannan bayanin ne, hukumar NIHSA ta Nijeriya ke tabbatar wa jama’a cewa su kwantar da hankalin su domin hakan ba zai jawo wata ambaliya ba sai dai sun umarci al’ummar da ke gaɓar kogin Benuwai su yi taka tsantsan.

Hukumar ta cigaba da cewa, a halin yanzu ba a tsammanin wata ambaliya saboda ruwan da ke kogin Benuwai ya na kan iyakoki amma duk da haka suna umartar jihohin da ke gaɓa da Kogin Benuwai su yi taka tsantsan. Jihohin sun haɗa da Adamawa, Taraba, Benuwai, Nasarawa, Kogi, Edo, Delta, Anambara, Bayelsa, Cross River da Ribas.

By ukarofi