Kashi 90 na masu safarar yara a Kano Hisba ke kamawa, ba NAPTIP ba – Malam Sufi

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta bayyana cewa kashi 90 na safarar yara da hukumar NAPTIP take yin nasara a kotu hukumar Hisba ce ta ke kamawa.

Darakta janar na hukumar ta jihar Kano, Malam Abba Sa’idu Sufi, da ya wakilci babban kwamandan Sheik Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana haka a yayin wata ziyara da Rundunar Ƴan kishin Kano RKK ta kai masa a hedkwatar hukumar ta jihar a ranar Talata da ta gabata.

A ɓangaren zamantakewar aure kuwa Mal. Sufi yace kashi 70 cikin ɗari na ayyukan hukumar ya ta’allaƙa ne ga harkar gyara auratayya da ke cikin al’umma, yayin da kashi 30 ya kasance sauran ayyukan ne na yau da kullum.

Ya kuma yaba da irin aikace aikacen da RKK ta ke aiwatarwa a Kano, sannan ya bada tabbacin cewa kofar hisba a buɗe take wajen haɗin gwiwa a kowane lokaci” a cewar Mal. Abba Sufi.

Tun da farko a jawabinsa shugaban Rundunar ƴan kishin Manjo Janar Ibrahim Sani Mai ritaya ya bayyana cewa babban dalilin ziyarar shi ne gabatar da hisba ƙungiyar ta RKK sannan su yaba mata da irin ƙoƙarin da hukumar take wajen ɗaukar matakin da ya dace akan lokaci.

Ya ƙara da cewa “Kamar yadda muka sani a da Kano ita ce ta ɗaya a Nijeriya da ma Afirka wajen kasuwanci amma a yanzu Kano ta koma wajen na bakwai zuwa ta 10 a Nijeriya.

“Babba burinmu Rundunar ƴan kishin Kano shi ne cicciɓa Jihar Kano mu ga ta koma matsayin da ta ke da shi a da na cinikayya da kuma riƙo da al’adu, Sannan mu na so mu dawo da martabar Kano a idon duniya ta yadda ko ina ɗan Kano ya je ya sha bamban da wanda ba ɗan Kano ba ta fuskar kyan hali da ɗabi’a kuma ina da yaƙini da haɗin gwiwa tsakaninmu da ku za mu cimma burin mu da izinin Allah” a cewa Janar Ibrahim Sani.

By ukarofi