
Daga BELLO A. BABAJI
Jami’an hukumar EFCC sun kai samame gidan gwamnatin jihar Kogi da ke Abuja don kama tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello.
Cikin wata sanarwa da Daraktan Ofishin Labaran tsohon gwamnan, Ohiare Michael ya fitar, ya ce jami’an sun je gidan ne don kamo mai gidan nasa wanda ya zarge su da yin harbe-harbe a lokacin kai samamen.
Haka na zuwa ne jim-kaɗan bayan Ohiare ya fitar da sanarwar cewa Yahaya Bello ya amsa gayyatar da hukumar ta yi masa inda bayan zuwan sa ofishin ne sai jami’an na EFCC suka ce masa ya tafi amma ya dawo a wani lokaci wanda bayan nan ne, sai jami’an suka kai farmaki a gidan gwamnatin jihar.
Ohiare ya ce, “mu na sanar da duniya cewa, matuƙar wani abu ya same shi, to EFCC za a tuhumta.”
A daren ranar Laraba ne EFCC ta ce Yahaya Bello ba ya ofishinta inda ta ce har yanzu ta na neman sa kan badaƙalar Naira biliyan 80.2 kamar yadda kakakinta, Dele Oyewale ya bayyana a cikin wata sanarwa.
A baya ne EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan kan zargin sa da hannu a cikin badaƙalar kuɗin wanda ya ƙi amsa gayyatar saboda waɗansu dalilai.
Kwanan nan ne, Mai Shari’a Emeka Nwite ya ɗage sauraron ƙarar tasa zuwa ranar 25 ga watan Satumba.
