Hukumar NGSA ta ce mutane kar su samu fargaba game da alamar girgizar ƙasa da aka yi a Babban Birnin Tarayya Abuja, inda ta shawarci mazauna garin kada su tashi hankalun su.
Sanarwa daga darakta-janar, Farfesa Olusegun Ige, ya bayyana cewa NGSA ta bibiyi girgizar ƙasan kuma ta gano cewa ba zai haifar da wata barazana ga muhalli ba.
“Binciken farko na siffofin ya nuna cewa tushen motsin ƙasan yana da nisan ƙasa da 5 km daga sashin bincike.
“Kungiyar NGSA ta kuma ziyarci yankunan da abin ya shafa domin tantance abubuwan da suka faru.
“Har ila yau, ƙarfin girgizar ƙasan wanda ya kai daga III – IV akan Ma’aunin Mercalli na Canzawa amma babu wata barazana game da haka.
“An shawarci mazauna Mpape, Katampe, Maitama da sauran wurare inda aka ji girgizar ƙasan kada su tashi hankalin su domin girgizar ƙasan gaba ɗaya a matsayin ƙanana ne.
“Hukumar tana ci gaba da binciken yanayin kuma za ta ba da sanarwa da zarar an samu wani canji.
“Har ila yau, ya kamata jama’a gaba ɗaya su sani cewa sashin binciken NGSA na cikin bincike a lokacin, don haka suna kira da al’ummar yankunan su kwantar da hankalin su domin babu wata matsala.
