Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bayyana cewa Nijeriya na kan gaba a fannin tattalin arziki ta ɓangaren Kasuwar Musulmi zalla da ake kira da Kasuwar halal ta duniya, wadda aka yi hasashen jarinta zai haura Dalar Amurka tiriliyan 7.7 a shekarar 2025
Kashim ya bayyana haka ne a wajen taron masu ruwa da tsaki na tattalin arzikin Halal da aka gudanar a dakin taro na Banquet Hall dake fadar shugaban ƙasa a Abuja a yau Laraba, 18/09/24
Mataimakin ya jaddada cewa girman tattalin arzikin Nijeriya da yawan al’ummarta yana samar mata da damammaki musamman a bangaren bunƙasa sashen saka hannun jari na halal.
Kasuwar Rumbun Halal wani shiri ne da ya ƙunshi sayar da ababen da addinin Musulunci ya halasta da suka haɗa da halatattun abinci da abin sha, da kayan kwalliya, da na gyaran jiki da yawon buɗe ido, har ma da takin zamani.
Mataimakin shugaban ya yaba wa kamfanoni masu zaman kansu saboda irin gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen tafiyar da tattalin arzikin na halal, musamman a fannin hada-hadar kuɗi, ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su haɗa hannu da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wajen samar wa da halal muhalli a Nijeriya.
Shettima, ya kuma jaddada buƙatar jawo hankulan masu zuba hannun jarin ƙasashen duniya, da faɗaɗa harkokin kasuwanci a yankin, da ƙara wayar da kan jama’a domin bunkasa Halali a Nijeriya.


