Ambaliyar ruwa da ambaliyar wuta!

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

A wannan makon ina son haɗa ambaliyar ruwa da ta shafi sassan Nijeriya musamman Maiduguri a Jihar Borno da kuma ambaliyar wuta da Isra’ila ke cigaba da yi a Zirin Gaza. Gaskiya hotunan da ke yawo a kafafen yanar gizo da su ka haɗa har da faya-fayan bidiyo na da ban tsoro na yadda ruwa ya malale birnin Maiduguri kai kace sassan tafkin Chadi ne. Hoton da ya fi ɗaukar hankali na shi ne na wani matashi da ya goyo mahaifin sa a baya duk da ba majanyi don kai shi tudun mun tsira daga cikin tsululun ruwan. Na ga an yi wa hoton taken “haihuwa ta yi rana” Mutane da su ka haɗa da malaman addini da shugabannin al’umma na isar da saƙonnin jaje da nuna raurawa kana bun da ya faru. Haƙiƙa abun damuwa ga duk wanda ya san dubban mutane da ke rayuwa a wannan babban birnin na arewa maso gabashin Nijeriya. 

Na tuna wata ambaliya a shekarun baya da ta auku a garin Gombe inda ruwa ya ruguza gidaje da dama da ma ɗauke mutane daga ɗakunan su yayin da wasu ke barci lokacin da ruwan ya zo. Mutane da dama sun rasa ran su. Ambaliyar ta Gombe ka iya zama da bambanci da Maiduguri don Gombe na da kwarurruka da ruwan kan bi ya wuce a taƙadirin lokaci inda ta nan kwarurrukan ma ruwa ya yi awun gaba da mutane da dukiya mai yawan gaske. Yadda na ga ambaliyar Maiduguri ruwan ya mamaye cikin gari ne da kan tituna inda mutane ke tafiya cikin ruwa. Gabanin ambaliyar ta shafi Maiduguri ta shafi wasu sassa na jihar Yobe inda dubban mutane su ka rasa matsuguni da hakan ya sa su ke buƙatar tallafin gwamnati da na sauran jama’a masu sukuni ko zuciyar tallafawa. Zai yi wuya a Nijeriya a samu ruwan damuna mai yawa ba tare da samun ambaliya ba. 

Ai ba ma sai a yankunan da a ke sa ran ambaliyar ba hatta a cikin babban birnin Nijeriya Abuja a kan samu ambaliya mai ban mamaki. Matuƙar an tafka ruwan sama za ka wasu titunan sun zama kamar fadamu inda za ka firgita wajen ratsa wasu yankunan ko da a cikin mota ne. Irin wannan fargaba ta fi tsanani a gangaren yankin Maraba jihar Nasarawa da ke makwabtaka da Abuja da tituna kan zama tamkar koguna ne da kan sa motoci su kafe ko injunan motocin ma su cije. Akwai lokacin da wani mai babur ma ya nitse a ruwan ya rasa ran sa a nan kan titin na Maraba wanda babbar hanya ce da ta haɗe Abuja da jihar Nasarawa zuwa sauran yankunan tsakiyar arewacin Nijeriya har arewa maso gabar. Shawara kawai in bai zama wajibi ba mutum ya ga haɗari ya nemi mafaka ya kuma gujewa hawa kan wasu tituna. 

Sai dai na lura cike magudanan ruwa a gefen titunan da shara kan sanya ruwan fantsama kan titi. Wani dalilin kuma shi ne gina gidaje kan magudanan ruwa ko ace hanyoyin ruwa. Hakan ya sa ya na da muhimmanci kafin mutum ya fara gini ya dau matakin tuntuɓar masana su duba ma sa filin kafin sanin mataki na gaba. Idan mutan Haɗejia na bin shafin nan su ma irin wannan ambaliyar ta shafi garin su a ’yan shekaru 3 da su ka wuce inda mutane su ka kwana su na aikin kafa shinge don dakatar da ruwan daga mamaye garin na arewa maso yamma. Ba mamaki yadda lamarin ya auku a Hadejia don yadda yankin ke da albarkar ruwa da fadamu. A bana ma ruwan ya shafi yankin Kafin Hausa inda mu ka samu labarin asarar da mazauna Bulangu su ka yi.

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ziyarci Maiduguri babban birnin jihar Borno don duba sassan da ambaliyar ruwa ya shafa.

Birnin dai tun a ƙarshen makwan jiya ya fara fuskankar barazanar ambaliyar inda ruwa ya shanye gidaje da daman gaske.

Kashim Shettima ya ce gagarumar ambaliyar ba a taɓa ganin ta ba tun fiye da shekaru 30 da su ka wuce.

Ambaliyar wacce ta malale farfajiyar fadar Shehun Borno mutane na tafiya tsundum cikin ruwa kamar kogi, ta shafi mutum 239,000 bisa alƙaluman majalisar ɗinkin duniya.

A nan Shettima da ya je Maiduguri bisa aiken shugaba Tinubu ya ce gwamnati za ta tallafawa waɗanda akasin ya shafa da lodin motoci cike da shinkafa 50.

Hakanan gwamnati inji mataikamin shugaban za ta haɗa kai da hukumar raya yankin arewa maso gabar don ƙarin taimako.

Mataimakin shugaban ya ce lamari ne da ya shafi sauyin yanayi inda dam ɗin Alau ya malalo don sassan rage ƙarfin sa sun zabce.

Dubban mutane sun koma zama a sansanonin gudun hijira kamar na Bakassi inda wasu kuma da ruwan ya ɗan janye su ka samu komawa gidajen su.

Ambaliyar ta shafi lamuran sadarwa, samar da ruwan sha da kuma makamashi kazalika da harkokin hada-hadar kasuwanci.

Ambaliyar wuta a Gaza:

Yankin Gaza kuma na cigaba da fuskantar ambaliyar wuta daga jiragen yaƙin Isra’ila da hakan kan yi sanadiyyar kisan gilla da mata da ƙananan yara. Duk batun neman tsagaita wuta ma ya zama soki burutsu don ba alamun dakatar da yakin daga ɓangaren Isra’ila.

Sojojin Isra’ila sun kara matsa lambar kai miyagun hare-hare kan yammacin gabar tekun Jodan inda gomman Falasdinawa su ka rasa ran su.

A hare-haren a arewacin gabar tekun bisa alƙaluman Falasdinawa ya baiyana mutuwar mutum 27.

Kazalika a Tukarem an samu harin jirgin saman yaƙi na Isra’ila da ya yi sanadiyyar kashe yaro mai shekaru 15.

A mako biyu da su ka gabata a yammacin kogin na Jodan an samu adadin Falasdinawa 30 da a ka kashe yayin da 130 su ka samu raunuka.

Mummunan harin Isra’ila kan Zirin Gaza a Jumma’ar da ta gabata ya yi sanadiyyar kisan gilla ga Falasdinawa 12.

Hare-hare a Nuseirat da ke cikin sansanoni 8 na gudun hijira a Gaza ya kashe mata biyu da yara biyu.

Wasu hare-haren a sauran sassan Gaza bisa bayanan jami’an kiwon lafiya sun yi sanadiyyar kisa ga Falasdinawa 12.

Wannan na faruwa ne lokacin da jami’an kiwon lafiya su ka dawo aikin  rigakafin cutar shan inna ga dubban yara.

Tankunan yaki na Isra’ila sun bazama yankin Khan Younis da Rafah a kan iyakar Masar da Gaza inda su ka ragargaza gidaje.

Mummunan hari da Isra’ila ta kai kan makarantar da majalisar ɗinkin duniya ke kula da ita a Gaza ya yi sanadiyyar kisan gilla ga kimanin mutum 34.

Harin dai ya shafi mazauna makarantar da ke zaman gudun hijira don yadda tuni boma-boman sojan Isra’ila su ka ruguzawa gidaje.

Cikin waɗanda su ka mutu bisa bayanan daga asibiti sun hada da mata 19 da kuma yara sai kimanin mutum 18 da su ka samu raunuka.

Cikin yaran da a ka kashe akwai ‘yar ɗaya daga jami’an agaji da ke aiki a arewacin Gaza mai suna Momin Selmi.

Jami’in agajin na taimakawa ne wajen ɗaukar waɗanda su ka samu raunuka da kuma tono waɗanda kan makale a karakshin gine-gine bayan harin boma-boma daga jiragen yaƙin Isra’ila. Selmi ya kai wata 10 bai ga ‘yar ta sa ba don ya na aikin taimakon ne a arewacin Gaza inda su kuma iyalinsa su ka yi hijira zuwa kudanci don gujewa hare-haren Isra’ila.

Isra’ila ta sha kai hare-hare kan makarantar da ke Nuseirat a tsakiyar Gaza da fakewa da cewa ta na farautar mayakan Hamas ne.

A rahoton da asusun yara na majalisar ɗinkin duniya UNICEF ya fitar ya nuna fiye da kashi 90% na makrantun Gaza sun samu dameji daga boma-boman Isra’ila yayin da fiye da rabin makarantun da ’yan gudun hijira ke samun mafaka sun fuskanci hare-hare daga sojojin Isra’ila.

Zuwa yanzu a yakin Gaza da Isra’ila ke yi da ya shiga wata 11 Falasdinawa dubu 41,084 su ka rasa ran su inda mutum dubu 95,029.

In za a tuna kutsawar ’yan Hamas a cikin Isra’ila a ranar 7 ga Oktobar bara ya yi sanadiyyar kisa ga Isra’ilawa 1,200 da sace kimanin mutum 270 ciki har da masu kasa biyu. Kun ga kenan daga fara maida martanin Isra’ila ta kashe ninkin-ba-ninkin na Falasɗinawa don fanshe mutum 1,200 ta kashe fiye da mutum 40,000. Hamas ta kai harin don kai wa iya wuya kan yadda Isra’ila ta mamaye ƙasar Falasɗinawa da yi wa Falasɗinawan kisan mummuke. Duk yunkurin da Afurka ta kudu ta yi wajen kai ƙarar Isra’ila kotun duniya don tuhumar kisan kare dangi bai dakatar da Isra’ila daga kai hare-haren ba. Hasalima Isra’ila ta furta kalmomin shaguɓe ko raini ga kotun kuma ta kwana lafiya. Gaskiya Isra’ila ce kusan ƙasar da kan yi abun da ta ga dama ta kwana lafiya.

Kammalawa;

Sauyin yanayi na daga abun da ke kwana ambaliyar ruwa don haka sai mutane sun bi shawarin masana don kaucewa abubuwan da kan kawo dumamar yanayi. Kazalika tabbatar da gujewa gine-gine kan hanyoyin da ruwa ke bi da kuma wajaje masu manyan madatsun ruwa da kan iya fashewa su fantsama cikin matsunan jama’a. Gwamnatoci a dukkan mataki ya dace su yi tsayin daka wajen kawo mafita ta hanyar tsara birane da kai ɗaukin gaggawa ga waɗanda iftila’i ya shafa.

By ukarofi