Dandalin Shawara: A binciken wayar mijina na gano yana tarayya da yayata ta jini

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Sunana………….daga nan……….dalilina na neman ki dai lamari ne ya kacame min. Wato Ina da ɗabi’ar ɗaukar wayar mijina na yi masa bincike idan ya shiga wanka ko idan yana bacci, amma bai san nakan yi ba. Ina yawan ganin mu’amalar sa da mata kala-kala, wani sa’in har kuka nake yi na ba kaina haƙuri.

To a cikin irin wannan lokacin wata ran na ga saƙwanin wata da suke yi da mijin nawa, da farko na ɗauka irin saura ce, sai daga baya na fahimci ta sanni, ta kan yi maganar tana tsoron na sani. Shi ne na ɗauki lambar na saka wayata, sai kau lambar ta nuna babbar yayata da muke uwa guda uba guda.

Na shiga tunani da damuwa sosai saidai ban san yadda zan iya zancen ba, don dole na faɗi yadda na gani, ga shi ana ta mana nasiha mu guji binciken wayar maza.

Ki ba ni shawara don gab nake da na kama da wuta, ban san ta yaya zan iya ci gaba da barin maganar a cikina ba. Na gode.

AMSA: Waalaiki salam. Da farko dai ba sai na ja da nisa akan binciken wayar miji ba, domin ko da ki ke yi kin san da yiwar ki gano abinda zai ɓata ranki. Saidai a nawa gani ba hujja ba ce da za ta sa maza su yi yadda suke so a ɓangaren mu’amalatar matan waje.

Ku sani ya ku maza, bai zama halal ba, yin mu’amala da mace ajnaba matuƙar ka san ba ka da niyyar yin aure, ya Allah ko don rashin hali, ko rashin sha’awar ƙarin auren. 

Ba ya daga cikin koyarwar addinin Muslumci namiji ya dinga soyayya da matan waje, alhali ba shi da niyyar aure. Anan ina maganar tsaftataciyyar soyayya ba ta shashanci ba.

Bai zama laifi ba idan kana da shirin ƙara aure ka nemi mace fiye da ɗaya ba don tantancewa, matuƙar dai da niyar auren ne, kuma ba wani haramtaccen abu da ke shiga tsakaninku.

Idan kuwa haka ne, ban ga inda shashancin da mata ke tarar wa a wayoyin mazajensu ya zama daidai ba. A ra’ayina, waɗanda ke yekuwan yi wa mata kashedi da binciken wayar mazaje zai fi su karkatar da hakan kan yi wa mazan nasiha su daina abinda suke yi.

Ba wai na ce mata masu duba wayar miji su na kyautawa ba, wannan aiki ne da za mu iya kira ‘jikinka ya gaya maka’, domin idan ki ka kai kanki, ke za ki kallo wa kanki abinda zai hana ki barci, kuma ba halin ɗaukar mataki don za a ce wa ya kai ki, kuma abin ƙarin haushi mijin naki ba ya dakuwa bare ki masa duka ki ji sanyi, kuma ba ya sakuwa bare ki danƙara masa saki ɗaya ya je gida ya koyo hankali. Idan kuwa haka ne, wa gari ya waya?

Kada mu saki layi, mu koma kan tambayar taki, tunda dai kin san binciken wayar mijin naki ba abin ƙwarai ba ne gare ki.

Zancen abinda ki ka gani da ya shafi ‘yar uwarki kuwa ba za ki iya haƙura ba, domin ba na jin akwai macen da za ta iya kawar da kai ga irin wannan ɗari bisa ɗari, a cigaba da rayuwa yadda aka saba. ɗayan biyun ne, ko dai ta yi shiru, abin ya yi ta cin ta har ya janyo mata ciwo, ko kuma ta fashe ƙurjin kome ta ke zama ta zama.

A nan shawarar da zan ba ki zan ce ki bi abin a hankali, ma’ana ki fara da tabbar da abinda ki ka gani yadda ki ke tsammani haka ɗin ne ba wani kokwanto. Idan kin yi wannan, sai ki koma ki samo hujja, domin irin wannan zance na fatar baki ba zai taɓa tasiri ba. Za ki samu hujja ne ta hanyar yin ‘screenshot’ na maganganunsu, inda yake ɗauke da lambarta a sama da duk wanda ya ɗauka zai iya gane ita ɗin ce.

To daga nan kina da zaɓi biyu, ko na ce ra’ayinki zai zama kashi biyu. Akwai yiwar kina da sha’awar fahimtar da mijinki kin sani, kuma ki kawar da alaƙar ba tare da wani ya sani ba. Ta nan za ki iya amfani da hujjar da ki ka samu, ki sanar da shi kin sani, ita ma ki yi mata hakan, tare da neman su janye alaƙar ko ki sanar da iyaye.

Hakan zai iya ba ki abinda ki ke so, wato raba su, musamman ma ta ɓangaren macen tunda ta fi kunyar duniya ta ji.

Idan kuwa iyaye ki ke son su shiga, nan ma da wannan hujjar za ki yi amfani, ki nemi duk abinda ki ke so daga wannan lamarin.

Abu na gaba, zan yi amfani da wannan damar na ba ki haƙuri, ki sani, kowanne bawa ana jarrabtar sa, duniyar bakiɗaya ma jarrabawa ce, kuma Shi mai jarrabta bayi, bai taɓa aiko wa bawanSa abinda ya san ba zai iya ɗauka ba. Don haka Ya san za ki ya ne shi ya sa Ya jarrabta ki. Kuma yadda za ki ɗauki lamarin, da irin hukuncin da za ki ɗauka, da hanyar da za ki ɗauke shi dukka suna cikin ababen da za a yi amfani wurin tabbatar da ke ci ko ke faɗi.

Duk wanda ya yarda Allah ne majibincin sa, to tabbas ba za ya taɓe ba. Ki koma ga Allah, ki nemi taimakonSa, ki gode masa, sannan ki nemi ya nuna maki hanyar da ta fi dacewa da ki bi don gudun saɓa masa.

Idan kin yi hakan, wallahi kina tare da nasara, domin wanda Allah Ya zama gatansa, tabbas shi ne asalin ɗan gata.

Daga ƙarahe ina kira ga maza da ku ji tsoron Allah. Ku tuna da hadisin ma’aiki (S.AW) da yake cewa, ” Imanin ɗayanku ba zai cika ba, har sai ya so wa ɗan uwansa abinda yake so wa kansa.” Ku tambaye kanku, ya za ku ji idan matanku suna abinda ku ke yi. Kada ku kafa hujja da cewa, namiji mijin mace huɗu ne, matuƙar ba da aure ka ke neman mace ba, to fa layinku ɗaya da matarka, laifinku ɗaya idan ka aikata saɓo.

Musulunci bai bambanta hukuncin mace mai aure idan ta yi zina da namiji mai aure idan ya yi zina ba. Dukkansu aka ce a jefe su.

Don haka idan ba ku da niyyar ƙari, ku gujewa kalle-kalle. Ku ƙyale ‘ya’yan mutane, don kuma za ku haifa, kuma za a yi wa naku abinda ku ka yi wa na wasu, ciki kuwa har da yaudara. Ka yi wa mace alƙawarin aure, alhali har a ranka ba ka da niyyar yin auren ko kuma auren wadda ka ke ɓata wa lokaci. Kawai kana nishaɗantuwa da zama da ita, ita kuwa ta amince da kalamanka na ƙarya har ta mayar da hankali ga iya kai kawai. Kaga kuwa akwai cutarwa.

Idan kuwa har da gaske ƙarin auren za a yi, to a guje ajiye ababen da uwargida za ta gani ranta ya ɓaci. Idan kana da adalci ko waya da wadda ka ke so ba za ka yi ba idan har kana cikin gidanka da matarka. Sannan ‘yan kalaman soyayyar nan a dinga gogewa ko taskace su ta yadda idan uwargida ba zai kai ba, matuƙar ba ita ta siyo wa kanta ba.

Mu tuwa, “Dukkanku makiyaya ne, kuma dukkanku abin tambaya ne akan abinda aka ba ku kiyo,” inji Manzon Rahma.

By ukarofi