
Daga UMAR GARBA a Katsina
A jiya Laraba, gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya kai ziyara jihar Borno don jajenta wa waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa.
A yayin ziyararsa, ya bai wa jihar Naira miliyan 100 don tallafa wa mutanen da ambaliyar ta rutsa da su.
Ya bayyana ambaliyar a matsayin wata jarabawa daga Allah (SWT) inda ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu yayin ambaliyar.
“Ambaliyar na ɗaya daga cikin ambaliyar ruwa mafi muni da ta taɓa faruwa a ƙasarmu, musamman a nan Borno. Mu na fatan Allah Ya kawo ɗauki tare da fatan Ya kare sake faruwar irin wannan iftila’i a kowane ɓangare na ƙasarmu.”
Da ya ke jawabi, gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna jin daɗinsa bisa ziyarar tare da gode wa al’umma da gwamnatin jihar Katsina bisa gudummuwar da aka bai wa jihar tasa.
Farfesa Zulum, ya kuma yi fatan cigaba da ɗorewar dangantaka tsakanin jihohin Nijeriya, musamman tsakanin Katsina da takwararta ta Borno.
Gwamna Raɗɗa ya samu rakiyar kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura; shugaban ma’aikatan Fadar gwamnatinsa, Hon. Jabiru Abdullahi Tsauri; Mai Martaba Sarkin Daura, Alh. Umar Faruk Umar da sauran su.
