
Daga BELLO A BABAJI
Ministan Labarai, Mohammed Idris ya shawarci ƴan Nijeriya su yi amfani da dama ta shirye-shirye da gwamnatin tarayya ke yi ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa.
Ministan ya faɗi hakan ne a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Laraba a taron wayar da kan al’umma game da shirye-shirye da gwamnati ta samar don inganta al’umma.
Jami’in hulɗa da jama’a na Ma’aikatar Labarai, Stanley Ugoeze wanda shi ya wakilci ministan a taron ya ce taron musamman an yi shi ne don wayar da kan ƴan ƙasa kan damanmaki da ke cikin shirye-shiryen da shugaban ƙasa ya samar.
Wasu daga ciki sun haɗa da tsare-tsare kamar haka; bai wa ɗalibai aron kuɗi, bada bashi ga kwastomomi, mallakar gas mai sauƙi, kasuwancin zamani, tallafin ƙanana da matsakaitan ƴan kasuwa da sauran su.
Ya kuma bayyana irin halin tsanani da Nijeriya da al’ummarta ke ciki, ya na mai cewa shugaban ƙasa ya samar da shirye-shiryen ne don al’umma su samu sauƙi da kuma riba.
A sakamakon haka ne ma’aikatar ta tsara taro irin wannan don wayar da kan al’umma game shirye-shiryen.
