An damfari bankunan Nijeriya biliyan N42.6 a wata uku – Rahoto

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Bankunan kasuwancin Nijeriya sun yi asarar Naira Biliyan 42.6 ta hanyar ’yan damfara da sauran ayyukan zamba tsakanin Afrilu da Yuni 2024, a cewar wani rahoto na baya-bayan nan.

An yi asarar wannan adadi ne a kashi na biyu na shekarar 2024 kaɗai, ya zarce yawan asarar da aka yi daga zamba a duk shekarar 2023, inda bankuna suka yi asarar Naira biliyan 9.4.

Rahoton ya samo asali ne kan zamba da shari’o’in jabu da cibiyoyin kuɗi 28 da ke ƙasar suka bayar.

FITC ta bayyana cewa an samu rahotanni 80 na zamba a cikin wannan shekarar, inda aka gabatar da ƙararraki 26 a watan Afrilu da kuma ƙararraki 27 kowanne a watan Mayu da Yuni.

Rahoton ya kuma yi nuni da yawan ayyukan damfara, inda ya aaru da kashi 1,784 daga N2.9 biliyan a farkon wannna shekara zuwa kusan biliyan N56.3 a cikin tsakiyar shekarar 2024.

By ukarofi