Kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United, Erik ten Hag ya yi watsi da kalaman tsohon tauraron ƙungiyar Cristiano Ronaldo inda ya ce shi fa ko kaɗan surutai daga waɗanda ba wasu a cikin United ba basa ɗaɗa shi da ƙasa.
Tun farko Ronaldo ya yi kakkausar suka ga Manajan bayan kalamansa da ke cewa ƙungiyar ba ta saran lashe ko wanne kofi a bana, inda ya ce sam irin kalaman bai kamata ya fito daga bakin Hag ba.
Duk da cewa shi kansa Ronaldon yayin wata hira da tsohon abokin wasanshi Rio Ferdinand ya bayyana cewa ba ya tunanin Manchester United ta iya lashe kofin zakarun Ingila, amma ya bayyana cewa abin kunya ne irin haka ta fito daga bakin manaja guda.
Manchester wadda rabonta da lashe kofin Firimiya tun shekarar 2013, idan har ta yi rashin nasara a hannun Southampton a wasanta na wannan mako kai tsaye za ta kafa tarihin faro kaka mafi muni bayan shan kaye a hannun Liɓerpool da Brighton.
A cewar Ten Hag, Ronaldon ya bayyana ra’ayinsa, wanda bai damu Manchester United ba, domin karya manta yanzu yana nesa da ƙungiyar ya na can Saudiya matsalar
Wannan kaka dai ka iya kasancewa mafi muni da Manchester United ta gani tun bayan makamanciyarta a kakar wasa ta 1986 zuwa 87 ƙarƙashin jagorancin Ron Atkinson wanda dalilin rashin nasarar ya tilasta korar shi tare da maye gurbinsa da Sir Aleɗ Ferguson.
Tsohon ɗan wasan gaba na ƙungiyar Manchester United Cristiano Ronaldo, ya soki salon jagorancin mai horas da ƙungiyar Erik ten Hag, inda ya ce ya kamata mamallaka ƙungiyar su yi dukkanin abinda ya kamata wajen sake fasalin yadda ake gudanar da ita a yanzu, don ci gaba da zama a sahun gaba a ɓangaren ƙwallon ƙafar Turai.
A yayin wata zantawa da Ronaldo ya yi da tsohon abokin wasansa Rio Ferdinand, ya ce kalaman mai horas da ƙungiyar na cewa ba zai iya lashe kofin Firimiya da kuma zakarun Turai ba, bai kamata ace sun fito daga mai horas da ƙungiyar ba.
Ronaldo ya ce lokaci ya yi da ya kamata ace an sake gina ƙungiyar yadda zata dawo da martabarta, wajen yin gogayya da takwarorinta a duniyar ƙwallon ƙafa.
Ya ce yana da tabbacin idan har Erik ten Hag zai saurari shawarwanin da Ruud ɓan Nistelrooy ke bashi, hakan zai taimaka masa matuka wajen samun nasarar ciyar da ƙungiyar gaba.
