Ahmed Musa bayyana aniyar dawowa gasar firimiyar Nijeriya

Spread the love

Kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa ya yi tsokaci kan yiwuwar komawa gasar firimiyar Nijeriya.

Musa ya buƙaci magoya bayansa da su yanke shawara a kan ƙungiyar da zai kasance a cikin ƙungiyoyi 20 na NPFL.

Tsohon ɗan wasan NPFL ya bayyana hakan a shafukan sada zumunta.

Musa ya rubuta a kan ɗ tare da tambarin ƙungiyoyin NPFL 20: “In sake komawa, wanne ƙunhiya ku ke so in sanya hannu a wannan a ciki.”

A baya Musa ya buga wasanni biyu da Kano Pillars a NPFL.

ɗan wasan mai shekaru 31 ya kasance ba shi da kulob tun bayan da ya bar kulob ɗin Siɓasspor na Turkiyya.

By ukarofi